NAJERIYA A YAU: ‘Yadda na yi kundumbalar ceto fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna’ -Tukur Mamu

Tattauna da Malam Tukur Manu kan shigarsa tsakani ’yan ta’adda da gwamnati don a sako fasinjijo jirgin kasan Abuja-Kaduna

NAJERIYA A YAU: ‘Yadda na yi kundumbalar ceto fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna’ -Tukur Mamu

Domin sauke shirin latsa nan

Shirin Najeriya A Yau ya yi tattaunawa ta musannan da Malam Tukur Manu kan yadda ya sayar da ransa wajen kubutar da fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna daga hannun ’yan ta’adda.

A ranar Babban Sallar nan ce Tukur Mamu ya je har maboyar ’yan bindigar suka sako mutum bakwai daga cikin fasinjojin — kari a kan 11 da suka saki a watan jiya.

NAJERIYA A YAU: Haduwar Ranakun Arafa Da Juma’a A Hajjin Bana

Zaman lafiya zai dawo Najeriya kafin Buhari ya bar mulki — Malami

Wasu a cikinsu sai da aka biya fansa aka sake su, wasu kuma haka nan ’yan ta’addan suka sake su.

Fiye da wata uku ke nan bayan  ’yan ta’adda sun yi garkuwa da fasinjoji 62 a harin da suka kai wa wani jirgin kasa da ke jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja a ranar 28 ga watan Maris na bana.

To sai dai har yanzu suna rike da ragowar fasinjojin, suna jira gwamnati ta biya wasu bukatunsu cikin har da sakin wasu daga cikin ’yan uwansu kafin su sako sauran fasinjojin.

Tun a watan Yunin ne dai wani mai suna Malam Tukur Mamu ya rika fadi-tashin shiga tsakani, da yin sulhu wajen ganin ’yan ta’addan sun sako fasinjojin.

Ga yadda tattaunawar shirin Najeriya A Yau ta kasance mai shiga tsakanin.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50