NAJERIYA A YAU: Yadda Ake Kamuwa Da Basir Da Hanyoyin Samun Waraka
shirin Najeriya A Yau ya yi duba ne kan cutar basir, abubuwan da ke kawo ta da hanyoyin da za a bi wajen magance ta.
Basir na daga cikin cututtukan da mutane da dama ke da mabanbantan ra’ayoyi a kanta.
A lokuta da dama, za ka ji yadda mutane ke faɗin dalilai daban-daban da ke janyo cutar basir, yayin da wasu ke ganin yawan zama ne ke kawo ta, wasu kuwa gani suke yi zaƙi da maiƙo ne ke kawo ta.
Wannan shi ne abun da da yawa daga cikin mutane suka sani kan wannan cuta, sai dai masana kiwon lafiya na da tasu fahimtar daban kan wannan cuta.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Azumi Ke Inganta Lafiyar Jiki
- DAGA LARABA: Taƙaddamar Da Ta Dabaibaye Zargin Sacewa Tare Mayar Da Walida Kirista
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai tattauna ne kan cutar basir da hanyoyin magance ta.
Domin sauke shirin, latsa nan