NAJERIYA A YAU: Yadda Cin Zarafin Mata Ya Zama Ƙarfen Ƙafa A Najeriya

Shirin Najeriya a Yau zai yi magana da matan da aka ci zarafinsu da ma mazan da suka ci zarafin matansu don gano bakin zaren.

NAJERIYA A YAU: Yadda Cin Zarafin Mata Ya Zama Ƙarfen Ƙafa A Najeriya

CIN ZARAFIN MATA

Cin zarafin mata a Najeriya matsala ce da ke ci gaba da ci wa masu ruwa da tsaki a ƙasar tuwo a ƙwarya.

Hanyoyin cin zarafin sun haɗa da lakaɗa musu duka da yi musu fyaɗe da wasu abubuwa da dama.

Ko wane irin hali mata suke shiga sakamakon cin zarafi a gidajen aurensu?

Shirin Najeriya a Yau zai yi magana da matan da aka ci zarafinsu da ma mazan da suka ci zarafin matansu don gano bakin zaren.

Domin sauke shirin, latsa nan