NAJERIYA A YAU: Yadda cire tallafin mai a Najeriya ya shafi makwabtanta
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio ya furta cewa wasu kasashen da ke makwaftaka da Najeriya suna jin radadin cire tallafin man da aka yi fiye ma da ‘yan kasar Najeriya.
Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio ya furta cewa wasu kasashen da ke makwabtaka da Najeriya na jin radadin cire tallafin man da aka yi fiye ma da ‘yan Najeriya.
Shirin namu na yau ya tsallaka kan iyaka ya shiga wasu kasashe makwabtan Najeriya domin mu ji ko abin da Shugaban Majalisar Dattawan ya fada da gaske.
- NAJERIYA A YAU: Musabbabin takaddamar siyasa a Jihar Filato
- Cire Tallafi: Majalisar Wakilai ta bukaci Tinubu ya fito da hanyoyin rage radadi
Shin ko cire tallafin mai a Najeriya ya shafi kasar Nijar?
Shirin ya tuntubi wani basarake a Accra, kasar Ghana, wanda ya bamu labarin mai a kasar.