NAJERIYA A YAU: Yadda Cutar Amai Da Gudawa Ta Yi Ajalin Mutum 25 A Sakkwato

Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai bi diddigin batun kisan mutane da cutar mai da gudawa ta yi a Jihar Sakkwato, don warware zare da abawa.

NAJERIYA A YAU: Yadda Cutar Amai Da Gudawa Ta Yi Ajalin Mutum 25 A Sakkwato

A ’yan kwanakin nan an samu rahotannin ɓullar cutar amai da gudawa a wasu sassan Jihar Sakkwato, inda aka ba da rahoton mutuwar mutum 25.

Kafafen yaɗa labarai da dama dai sun fitar da rahotanni kan wannan al’amari da ya tayar da hankulan al’umma a ciki da wajen jihar.

Sai dai kuma hukumomi sun ce wannan adadin na waɗanda cutar ta yi ajalinsu daga watan Janairu ne zuwa yanzu.

Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai bi diddigin lamarin don warware zare da abawa.

Domin sauke shirin, latsa nan

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025