NAJERIYA A YAU: Yadda Dan Chana Ya ce Ya Kashewa Ummita Miliyan N120

Cikakken bayanin abin da ya faru a kotu da ma wadansu batutuwa.

NAJERIYA A YAU: Yadda Dan Chana Ya ce Ya Kashewa Ummita Miliyan N120

Wanda ake zargi da kashe Ummita yayin fitowa daga Kotu

A ci gaba da sauraron karar kisan gillar da ake  zargin  wani dan kasar Chana da yi wa wata bakanuwa (Ummita), wanda ake zargin ya bayyana yadda ya kashe wa marigayiyar miliyoyin Naira.

Ko kun san a ikirarin dan Chana harda bayyana cewa ya na baiwa marigayiya Ummita alawus din Naira dubu dari duk mako?

Shirin Najeriya  A Yau na wannan lokaci na dauke da cikakken bayanin abin da ya wakana a kotu, da ma wadansu batutuwa.