NAJERIYA A YAU: Abin da Abba Kyari Ya Fada Kafin A Kama Shi
Bayanin zargin fasakwaurin miyayun kwayoyi da ake wa fitaccen dan sanda mai yaki da da masu garkuwa da mutane
DCP Abba Kyari
Domin sauke shirin latsa nan
Bayyanar suna da hotunan hafsan dan sandan nan da ya yi fice wajen yaki da masu garkuwa da mutane, DCP Abba Kyari, a matsayin wanda ke da hannu a safarar miyagun kwayoyi ya dauki hankalin ’yan Najeriya.
’Yan kasar sun rabu tsakanin masu gaskata bidiyon da masu ganin kirkirar sa aka yi saboda .
Tun a kwanakin baya dai DCP Abba Kyari ya shiga tsaka mai wuya a zargin a badakalar damfarar miliyoyin daloli da Hushpuppi ya yi a kasashen waje.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da cikakken bayanin yadda aka haihu a ragaya.