NAJERIYA A YAU: Yadda Kanawa Ke Gwara Kawunan Su Akan Hotunan Sarakuna

Ana ganin Sarki Sanusin na ɗasawa da gwamnatin Jihar

NAJERIYA A YAU: Yadda Kanawa Ke Gwara Kawunan Su Akan Hotunan Sarakuna

Sarkin Kano na 14, Sanusi Lamiɗo Sanusi II

Ganin hotunan Sarki Muhammadu Sanusi na II a ɗakin taron fadar Gwamnatin Jihar Kano ya jawo zargin shirin dawo da shi kan karagar mulki bayan shekara uku da tube shi daga sarautar, kamar wasu ake hasashen Gwamna Abba Kabir Yusuf zai yi.

Lamarin dai ya yi ta jawo ce-ce-ku-ce, musamman ganin Sanusin na ɗasawa da gwamnati mai ci a jihar; Shin a ina gizo ke saka?

A cikin shirin Najeriya A Yau, mun nemi gano duba ainihin musabbabin maƙala hoton Sanusin a ɗakin taron na gidan gwamnati a gefen hoton shugaban kasa da na gwamna mai ci.

Domin sauraren shirin ko sauke shi kai-tsaye, a lasta nan