NAJERIYA A YAU: Yadda Kasuwannin Zamanin Gwamnoni Ke Karya ’Yan Kasuwa
’Yan kasuwa na kukan cewa tsadar shagunan a kasuwannin da gwamnoni suka gina ta fi ƙarfinsu, ga shi kuma an raba su da inda a baya suke gudanar da kasuwancinsu
Gwamnatocin jihohi da dama sun rushe kasuwanni inda suka gina sabbi na zamani.
Sai dai ’yan kasuwar da gwamnatocin suka tayar daga wuraren da a baya suke gudanar da harkokinsu domin gina kasuwannin zamanin na kukan cewa sabbin kasuwannin sun fi ƙarfin su, domin kuwa ba sa iya mallakar shaguna a ciki.
Shirin Najeriya A Yau ya duba yadda ’yan kasuwar da abin ya shafa suke ci gaba da gudanar da rayuwa.
Domin sauke shirin, latsa nan