NAJERIYA A YAU: Yadda Kiristoci Ke Gudanar Da Bikin Kirsimeti A Cikin Musulmi
Yadda kiristoci ke gudanar da bukukuwan kiristimeti a cikin Musulmai da yadda dangantaka ke kasancewa tsakaninsu.
A duk faɗin Arewacin Najeriya, ana gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna, duk da kasancewar Musulmai ne suka fi rinjaye a yawancin yankuna. Kiristoci kan yi bukukuwansu cikin mutunta al’adar Musulmai, yayin da Musulmai kuma ke nuna goyon baya ta hanyar gaisuwa, da tsaro, da mu’amala ta zamantakewa.
A wurare da dama kamar Kaduna, Jos, Zaria, Minna da wasu sassan jihar Kano, ana ganin Kiristoci suna zuwa coci ba tare da tsangwama ba, yara suna yin nishadi tare, makwabta suna raba abinci da gaisuwar biki. Wannan yanayi na nuna cewa zaman lafiya, girmamawa da zumunci sun fi bambancin addini ƙarfi a rayuwar yau da kullum ta Arewacin Najeriya.
- NAJERIYA A YAU: ‘Halin Kunci Da Muke Ciki A Sansanin Gudun Hijira Yayin Bikin Kirsimeti’
- DAGA LARABA: Yadda Ragin Farashin Man Fetur Zai Shafi Rayuwar ‘Yan Najeriya
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan yadda kiristoci ke gudanar da bikin kirsimeti a tsakiyar musulmai.
Domin sauke shirin, latsa nan