NAJERIYA A YAU: Yadda Kuɗin Crypto Zai Haɓaka Tattalin Arzikin Najeriya

Alfanun da ’yan Najeriya za su iya samu daga kuɗin crypto, musamman tun bayan zaɓen Donald Trump a matsayin Shugaban Ƙasar Amurka a karo na biyu.

NAJERIYA A YAU: Yadda Kuɗin Crypto Zai Haɓaka Tattalin Arzikin Najeriya

e-naira

Kudaden crypto na cikin hanyoyin da zamani ya zo da su da nufin sauƙaƙa hada-hada a tsakanin al’umma, musamman a ƙasashen da suka ci gaba.

Sai dai a Najeriya, har yanzu ba kowa ne ya san wannan harka da kuma yadda ya kamata a yi ta ba, musamman duba da yadda kuɗin na crypto  ya yi daraja a faɗin duniya.

Shirin Najeriya a Yau na wannan lokacin zai yi nazari ne a kan alfanun da ’yan Najeriya za su iya samu daga kuɗin crypto, musamman tun bayan zaɓen Donald Trump a matsayin Shugaban Ƙasar Amurka a karo na biyu.

Domin sauke shirin, latsa nan