NAJERIYA A YAU: Yadda Kuɗin Kujera Yake Neman Hana Maniyyata Sauke Farali

Saura mako biyu wa’adin kammala biyan kuɗin kujerar aikin Hajjin bana, amma maniyyata ’yan ƙalilan ne suka iya biya

NAJERIYA A YAU: Yadda Kuɗin Kujera Yake Neman Hana Maniyyata Sauke Farali

Yanzu haka, saura mako biyu wa’adin da aka ɗebar wa maniyyata Hajjin bana su biya kudin kujerar ya cika, amma rahotanni daga wasu sassan ƙasar nan na nuna cewa ƙalilan ne suka iya biya.

Kudin kujerar Hajjin ya tsorata ’yan Najeriya a bana, bayan da hukumomi suka ce duk mai sha’awar sauke farali sai ya biya kudi sama da Naira miliyan takwas.

Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan