NAJERIYA A YAU: Yadda Kudin Crypto Ya Sanya Matasa Yin Saki-Na-Dafe

Halin da matasa suka tsinci kansu bayan sun yi ‘mining’ ɗin Hamster

NAJERIYA A YAU: Yadda Kudin Crypto Ya Sanya Matasa Yin Saki-Na-Dafe

Matasa da dama a Najeriya ne suka yi sake-reshe-kama-ganye saboda hangen dala.

Tunanin samun kudi masu yawa ta hanyar kudin kirifto na Hamster, ya sa John Adams ya yi murabus daga aikinsa, daga ƙarshe ya tashi ba shi ga tsuntsu, ba shi ba tarko – ma’ana, babu aikin babu kuɗin.

Shirin Najeriya A Yau zai tattauna ne a kan halin da irin waɗannan matasa suka tsinci kansu bayan mining din Hamster.

Domin Sauke shirin, latsa nan

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara