NAJERIYA A YAU: Yadda ma’aikata za su daina jira kafin shigowar albashin watan Janairu

Watan Janairu kan zo da ƙalubale kasancewar an biya masu aikin albashi da wuri a cikin watan Disamba, sun kuma ƙarar da shi a kan bukukuwan da ƙarshen shekara

NAJERIYA A YAU: Yadda ma’aikata za su daina jira kafin shigowar albashin watan Janairu

A duk lokacin da aka ce an biya albashi, yanayi kan sauya ga masu karɓa har da masu sana’o’i a kasuwanni da ƙananan shaguna a unguwanni.

Sai dai watan Janairun kowace shekara kan zo da ƙalubale kasancewar an biya masu aikin albashi da wuri a cikin watan Disamba, sun kuma ƙarar da shi a kan bukukuwan da watan kanzo da su.

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan yadda masu aikin albashi za su kauce wa shiga halin ni-’ya-su kafin biyan albashin watan Janairu

Domin sauke shirin, latsa nan