NAJERIYA A YAU: Yadda masu yi wa kasa hidima za su ci arzikin yankunan da suke aiki
shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci yayi nazari ne kan irin damar da masu hidimtawa kasa suke dasu na samun aiki, koyon sana’a ko saka hannun jari a garuruwan da aka tura su.
Matasa Masu Yi Wa Kasa Hidima
Bayan hadin kai da karfafa fahimtar juna wadanda hidimar kasa take kawowa, akan samu wasu masu hidimar da sukan yi amfani da duk wata dama da suka samu don neman na sakawa a bakin salati.
Yayin da wasu masu hidimar kasa sukan kama sana’a ko su saka hannun jari a inda aka tura su, wasu kuwa komawa garuruwansu suke yi bayan sun kammala.
- NAJERIYA A YAU: Cututtukan da rumar daki ke haifarwa ga jikin mutum
- DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan irin damar da masu yi wa kasa hidima suke da ita a garuruwan da aka tura su.
Domin sauke shirin, latsa nan