NAJERIYA A YAU: Yadda Rashin Ɗaukar Darasi Ya Haddasa Gagarumin Asara A Suleja
Ko me ya sa ya sa har yanzu ’yan Najeriya ba su shiga taitayin su ba da zuwa ɗibar man fetur idan tanka ta fadi?
Ƙiyasi ya nuna cewa an yi asarar miliyoyin Naira bayan da shaguna maƙare da kayayyaki da motocin hawa da na haya suka ƙone ƙurmus, uwa uba kuma rayuka aƙalla 80 suka salwanta sakamakon fashewar tankar mai a Marabar Dikko da ke kusa Suleja a Jihar Neja.
Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da faɗuwar tankar mai ta haddasa asarar dukiya da rayukan mutane masu yawa.
Ko me ya sa ya sa har yanzu ’yan Najeriya ba su shiga taitayin su ba da zuwa ɗibar man fetur idan tanka ta fadi?
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Suka Sa Farashin Citta Ta Yi Tashin Gwauron Zabo
- DAGA LARABA: Dalilan ɓaraka a tsakanin iyayen riƙo da ’ya’yan riƙo
Wannan ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokacin zai tattauna a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan