Najeriya A Yau: Yadda Tinubu da Dattawan Arewa Suka Yamutsa Hazo Kan Zaben 2023
Dalilan Tinubu na bayyana aniyar takararsa a Fadar Shugaban Kasa da kuma wanda Kungiyar Dattawan Arewa ke son ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Domin sauke shirin latsa nan
Bayyana aniyar takarar shugaban kasa a zaben 2023 da Bola Ahmed Tinubu ya yi a Fadar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta tayar da kura a fagen siyasar Najeriya.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya zakulo dalilan Tinubu na bayyana maganar takarar tasa a Fadar Shugaban Kasa da kuma matsayar Kungiyar Dattawan Arewa dangane da wanda suke son ya yi takarar shugaban kasa a zaben 2023.