NAJERIYA A YAU: Yadda Tsarin Ilimi Ke Karya Gwiwar ’Yan Najeriya
Daya daga cikin dalilan dake karya gwiwar matasana Najeriya wurin neman ilimi shine yadda baka iya bambance wanda ya yi ilimi da wanda bai yi ba wajen samun damarmaki.
Wasu dalibai ke jiran daukar darasi a cikin ajinsu a Kwalejin Sardauna Memorial College da ke Kaduna ranar Litinin.
Hoto daga Shehu K. Goro
’Yan Najeriya da dama ne dai da suka yi ilimin zamani dole ta sa suka rungumi sana’o’in da a baya ake ganin na kaskantattu ne don su samu na sakawa a bakin salati.
Mai yiwuwa hakan ne ya sa wasu, musamman matasa, suka yanke kauna da cewa shafe lokaci ana karatun kan iya taimaka wa mutum magance bukatunsa nay au da kullum.
- NAJERIYA A YAU: Me ya sa mutane suka dawo daga rakiyar Kirifto?
- DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya A Najeriya
Wannan shi ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan