NAJERIYA A YAU: Yadda Wahalar Fetur Ke Jigata ’Yan Najeriya
Karancin man fetur na neman tsayar da al’amura cak ga al’umma a wasu sassan Najeriya.

Karancin man fetur na neman tsayar da harkokin cak ga al’umma a sassan Najeriya.
Mutane da dama sun ce lamarin ya shafe su kai-tsaye kuma suna dandana kudarsu.
Shin yaushe wannan matsala za ta kawo karshe, lura da cewa Kamafanin Mai Na Kasa (NNPC) ya ce ya riga maganace ta?
A shirin Najeriya a Yau mun tattauna da wadanda abin ya shafa sannan mun ji ta bakin masu ruwa da tsaki kan yiwuwar samun mafita nan kusa.