NAJERIYA A YAU: Yadda Wata Bakuwar Cuta Take Cin Naman Jikin Mutanen Malabu
Yadda baƙuwar cutar take yaɗuwa da matakan da ya kamata a ɗauka don kauce wa kamuwa da ita.
Wata cuta mai cin naman jikin dan Adam ta yi sanadin mutuwar mutum takwas yayin da wasu fiye da 60 suke kwance a asibiti a garin Malabu da ke Karamar Hukumar Fufure ta Jihar Adamawa.
Wannan lamari dai ya jefa fargaba a zukatan mazauna yankin.
- NAJERIYA A YAU: Ayyukan Da Fasahar AI Za Ta Raba Mutane Da Su Nan Ba Da Jimawa Ba
- DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi bincike a kan yadda wannan cuta take yaɗuwa da matakan da ya kamata a ɗauka don kauce wa kamuwa da ita.
Domin sauke shirin, latsa nan