NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Najeriya Suka Jure Wa Matsin 2024
Waɗannan manufofi sun haɗa da janye tallafin man fetur da ƙyale kasuwa ta yi halinta a kan darajar Naira da janye tallafin wutar lantarki da sauran su
Tun bayan rantsar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a watan Mayun bara ne dai ’yan Najeriya suke ta kokawa da matsin tattalin arziki sakamakon wasu tsare-tsare da manufofi da Gwamnatin Tarayya ta bijiro da su.
Waɗannan manufofi sun haɗa da janye tallafin man fetur da ƙyale kasuwa ta yi halinta a kan darajar Naira da janye tallafin wutar lantarki da sauran su.
- NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Lamari Game Da Harin Sojoji Kan Al’umma A Sakkwato
- DAGA LARABA: Dalilan da wasu darikun Kirista ba sa bikin Kirsimeti
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi tsokaci ne a kan jimirin da ’yan Najeriya suka yi a shekarar.
Domin sauke shirin, latsa nan