NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Ribaci Kwanaki Goma Na Karshen Ramadan

Yadda ake ibada domin dacewa da daren Lailatun Kadar da wasu falalolin goman karshe na watan Ramadan

NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Ribaci Kwanaki Goma Na Karshen Ramadan

Domin sauke shirin latsa nan

Musulmin duniya baki daya na hankoron dacewa da falalar kwanaki goman karshe na watan azumin Ramadan.

Sanin cewa a cikin wadannan kwanaki goma na karshen Ramadan ake riskan daren “Lailatul Kadari”, kirdadon wannan dare na sa Musulmin dagewa da ayyukan ibada.

Wadanne ibadu aka fi son a yawaita a wadannan kwanaki masu alfarma?