NAJERIYA A YAU: Yadda za ka dauki mataki idan aka bata maka suna saboda cin bashi
Kamfanonin bayar da bashin kan aika saƙonnin cin zarafi da barazana har ga ’yan uwa wanda ya ci bashi ta manhajojinsu
A wannan zamani mutum zai iya samun bashi kai-tsaye ta waya daga manhajoji, amma idan ya kasa biya kamfanonin da da suka ba da bashin sukan aika masa sakonnin cin zarafi da barazana har ga ’yan uwansa.
Duk da gargadin da hukumomi ke yi, mutane da dama na kukan cewa ana ɓata musu suna, kuma an kasa kulle irin wadannan manhajoji, kamar yadda aka ce.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Gwamnati Ke Nufi Da Iya Kwazonka, Iya Albashinka
- DAGA LARABA: Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mai Aikin Hajji
Shirin Najeriya a Yau ya tattauna yadda aka kasa daukar matakin dakatar da manhajoji cin bashi da kuma matakin da ya kamata mutum ya dauka idan hakan ta faru.
Domin sauke shirin, latsa nan