NAJERIYA A YAU: Yadda Za Ku Ceto Yaron Da Ya Kamu Da Jijjiga
Yanayin yana kama da farfadiya amma masana sun bayyana bambancin da ke tsakaninsu
Shin kun taba cin karo da yara masu jijjiga? Wani yanayi ne da larurar kwakwalwa ko kasancewar guba a cikin jini da zazzabi mai tsanani kan haifar wa yara.
Yanayin kan sa yaro ya samu sarkewar gabobin jiki da numfashi kamar mai farfadiya a wasu lokutan.
- NAJERIYA A YAU: Yadda za ka dauki mataki idan aka bata maka suna saboda cin bashi
- DAGA LARABA: Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mai Aikin Hajji
Shirin Najeriya a Yau na dauke labarin wata matar da irin hakan ya faru ga ’yarta har ma da shawarwarin masana game da alamomin da za ku gane irin wannan yanayi da kuma matakin da za ku iya dauka idan hakan ta faru.
Domin sauke shirin, latsa nan