Yadda IPOB Da ’Yan Siyasa Ke Wasan ‘Buya’ A Anambra
Zaben gwamna ya matso amma ’yan siyasa da mazu zabe na firgice, INEC kuma ta ce sai an yi zaben.
‘Yan awaren Biyafara na IPOB
Domin sauke shirin latsa nan.
A yayin da zaben gwamna ke kara matsowa, ’yan siyasa sun shiga buya saboda tsoron ’ya’yan haramtacciyar kungiyar IPOB a Jihar Anambra.
- Najeriya A Yau: Shin Najeriya kasa ce mai ’yanci?
- Daga Laraba: Dalilan mutuwar kishin kasa a zukatan ’Yan Najeriya
Mazauna jihar, wadanda kuma zu ne masu jefa kuri’a na cikin zullumi, ganin yaddan IPOB din ke kara kai hare-hare a yankin na Kudancin Najeriya.
Shin yaya ’yan siyasar jihar ke gudanar da yakin neman zaben gwamnan a irin halin da ake ciki, ganin cewa hukumar zabe ta kasa (INEC) ta ce babu makawa sai an gudar da zaben, nan da mako biyar.
Wannan shi ne batun da a yau shirin namu zai mayar da hankali a kai.