NAJERIYA A YAU: ‘Za Mu Daure Duk Wanda Bai Yi Gwajin Jini Kafin Aure Ba’
Sabuwar dokar da gwamnatin jihar Kano ta sanya wa hannu na shan yabo da suka.

Abba Kabir Yusuf
Sabuwar dokar da gwamnatin jihar Kano ta sanya wa hannu kan yin gwajin lafiya kafin aure na shan yabo da suka.
A cewar gwamnatin, yawaitar yaduwar cututuka a tsakanin ma’aurata bayan aure shi ne musabbabin yin dokar.
Amma me ya sa za a daure wanda ya taka dokar tsawon shekara biyar ko a yi masa tarar 500,000?
Idan aka taka dokar wa za a daure tsakanin mijin da mata ko madaurin auren?
- NAJERIYA A YAU: Abun Da Za A Fara Lura Kafin Shiga Tasi A Abuja
- DAGA LARABA: Dalilan Da Za A Hana ’yan kasa da shekara 18 shiga jami’a
Shirin Najeriya a Yau ya zanta da masu ruwa da tsaki da masana shari’a kan wannan doka.
Domin sauke shirin, latsa nan