Najeriya ba ta amfani da yawan al’ummarta wajen bunkasa tallalin arzikinta – Dangote
Shugaban Rukunin Kamfanonin dangote, Alhaji Aliko dangote, ya nuna damuwa kan yadda Najeriya ta gaza yin amfani da damar da take da ita ta yawan jama’a, wajen habaka tattalin arzirkinta. Alhaji Aliko dangote, wanda Babban Daraktan Rukunin Kamafanonin, Alhaji Ahmed Mansur ya wakilta a yayin wani taron kaddamar da sashen kasuwanci na Jami’ar Ibadan, mai […]
Shugaban Rukunin Kamfanonin dangote, Alhaji Aliko dangote, ya nuna damuwa kan yadda Najeriya ta gaza yin amfani da damar da take da ita ta yawan jama’a, wajen habaka tattalin arzirkinta.
Alhaji Aliko dangote, wanda Babban Daraktan Rukunin Kamafanonin, Alhaji Ahmed Mansur ya wakilta a yayin wani taron kaddamar da sashen kasuwanci na Jami’ar Ibadan, mai taken ‘Rawar da Masana’antu ke takawa wajen ciyar da tattalin arzikin kasa gaba”, ya kara nuna mamakinsa a kan yadda aka yi wasti da kayayyakinmu na gida aka raja’a a kan kayyyakin da ake shigowa da su daga waje.
Yana wannan magana ce jim kadan bayan gudunmawar musamman ga ci gaba da tafiyar da wannan tsangaya ta kasuwanci a jami’ar, inda ya yi nuni da cewar Najeriya tana kashe sama da Naira tiriliyan 1 da rabi duk shekara wajen shigo da abinci, kuma hakan yana kara zama nauyi ga asusun ajiyar waje.
Ya kara da cewa, kashi 80 bisa 100 na kayan mafi yawanci ana sarrafa su a Najeriya, amma har yanzu an dogara a kan kayan da ake shigowa da su cikin kasar nan, inda ya yi nuni da cewa Kamfanin dangote yana samun ci baya wajen samar da tsari, duk da gudunmawar da kamfanin ke bayarwa wajen ciyar da tattalin arzikin kasar nan gaba.
A karshe dangote ya ce, idan aka yi la’akari da yawan al’ummar Najeriya da kuma irin dimbin ma’adananta na karkashin kasa, za a ga wata baiwa ce da ba dukan kasashe suke da hakan ba, musamman wajen sarrafa kaya.