Najeriya ba ta kai matsayin fara yanke hukuncin kisa a kan laifin cin hanci ba – Shugaban NIPSS
Ya ce canjin dabi’u ake bukata ba hukuncin ba
Shugaban Cibiyar Bayar da Horo kan Harkokin Mulki ta Najeriya (NIPSS), Farfesa Ayo Omotayo, ya ce gar yanzu Najeriya ba ta kai matsayin da za ta iya fara zartar da hukuncin kisa kan masu cin hanci da rashawa ba.
Ya bayyana haka ne ranar Alhamis a Abuja yayin wani taro da cibiyar ta shirya a kan farfado da hanyoyin gyara dabi’un jama’a kan cin hanci a hukumomin gwamnati da masu zaman kansu a kasar nan.
- Gwamnatin Kano ta haramta amfani da littafin ‘Queen Primer’ saboda lalata tarbiya
- Saudiyya ta miƙa tayin karɓar baƙuncin Gasar Kofin Duniya ta 2034
A cewarsa, “Cin hanci mataki-mataki ne. Idan dan sanda ya karbi N100 daga hannunka, wannan cin hanci ne, amma shin hakan na nufin za ka yanke wa mutum hukuncin kisa saboda karbar N100? Saboda haka rashawa ma mataki ce.
“Kazalika, ba zai yiwu mu goyi bayan a fara yanke hukuncin ba. Muna kan wani matsayi ne da canjin dabi’u muke bukata domin mu magance cin hanci.
“Mun yi imanin idan za mu iya rage ko da rabin cin hancin da yake a Najeriya ne, kasarmu za ta bunkasa,” in ji shi.
Shugaban ya kuma ce hanya mafi sauki da za a iya canza dabi’un mutane ita ce ta hanyar ilimi, inda ya ce dalili ke nan ma da suka shirya taron.
Shi ma da yake bayani a wajen gabatarwar, Shugaban Kungiyar Jam’iyyun Siyasa ta Najeriya (IPAC) yabagi Yusuf Sani, ya ce duka sadarorin cikin kundin na da alaka da jam’iyyun siyasa.