Najeriya ba za ta taba amincewa da auren jinsi ba – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shaida wa mahukuntan Amurka cewa Najeriya ba za ta taba amincewa da auren jinsi ba.Mashawarcin Shugaban kas kan Al’amuran Watsa Labarai Mista Femi Adesina ne ya bayyana haka a shafinsa na Tweeter a shekaranjiya Laraba.Shugaba Buhari wanda ya dawo gida a jiya Alhamis bayan amsa gayyatar Shugaba Barack Obama, Adesina […]

Najeriya ba za ta taba amincewa da auren jinsi ba – Buhari
Najeriya ba za ta taba amincewa da auren jinsi ba – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shaida wa mahukuntan Amurka cewa Najeriya ba za ta taba amincewa da auren jinsi ba.
Mashawarcin Shugaban kas kan Al’amuran Watsa Labarai Mista Femi Adesina ne ya bayyana haka a shafinsa na Tweeter a shekaranjiya Laraba.
Shugaba Buhari wanda ya dawo gida a jiya Alhamis bayan amsa gayyatar Shugaba Barack Obama, Adesina ya ruwaito shi yana shaida wa mahukuntan Amurka ga-da-ga a ranar Talata cewa ba ma auren jinsi ya saba wa doka kawai ba ne a Najeriya, har ma ya zama abin kyama ne ga al’adun mutanen kasar.
“Batun auren jinsi ya taso jiya (ranar Talata) a nan. Kuma Shugaba Buhari kai-tsaye ya ce namiji ya nemi namiji ko mace ta nemi mace ya saba wa dokokin Najeriya, kuma abin kyama ne a ala’du da addinanmu,” inji Kakakin Shugaban kasar.
Kafin Shugaban kasa Buhari ya bar kasar nan a ranar Lahadi ’yan Najeriya da dama ciki har da kungoyoyin fararen hula da na kare hakkin dan Adam sun bukaci ya yi watsi da duk wani yunkuri na takwaransa na Amurka na tilasta halatta auren jinsi a Najeriya.
A shekarar 2013 ne Majalisar Dattawa ta mayar da luwadi da madigo da auren jinsi babban laifi, inda ta bayyana su da bakin al’adu ne a kasar nan.