Najeriya ba za ta wargaje a hannuna ba – Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana kiraye-kirayen da wasu daidaiku da kungiyoyi ke yi game da sake fasalin Najeriya ba komai ba ne face rashin hange da kuma yunkurin wargaza kasar. Sannan ya sha alwashin cewa hakan ba za ta faru a karkashin jagorancinsa ba. Shugaban ya bayyana hakan ne ranar Lahadin da ya gabata a […]

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana kiraye-kirayen da wasu daidaiku da kungiyoyi ke yi game da sake fasalin Najeriya ba komai ba ne face rashin hange da kuma yunkurin wargaza kasar. Sannan ya sha alwashin cewa hakan ba za ta faru a karkashin jagorancinsa ba.
Shugaban ya bayyana hakan ne ranar Lahadin da ya gabata a jawabinsa na bikin cika shekara 57 da samun ‘yancin Najeriya. Ya yi dogon bayani inda ya nuna cewa ba zai taba amincewa da kiraye-kirayen da wadansu ‘yan Najeriyar ke yi na yunkurin ballewa ba.
“A lokacin da nake matashin soja, na ba da gudummuwata tun daga farko har karshen yakin Basasar Najeriya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da miliyan biyu, ya kuma haddasa asarar dukiyoyi da barna mai yawan gaske,” in ji Shugaba Buhari.
Ya ci gaba da cewa wadanda suke kiraye-kirayen maimaita hakan a yanzu “ba a haife su ba lokacin yakin, don haka ba su da masaniya game munanan abubuwan da yakin ya haifar wa al’ummar Najeriya.”
Haka zalika Shugaba Buhari ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda wadansu jagorori a yankin da ke son ballewar, yana mai cewa “Ba sa jan kunnen matasan yankin nasu wadanda suke ci gaba da hankoran a raba Najeriyar.”
Koda yake shugaban ya ce sulhu shi ne mafita kan duk wani al’amari. Sannan sai ya bukaci dukkan wanda yake da wani korafi game da kasar da ya gabatar da shi ga majalisar dokoki ta tarayya da kuma majalisun dokoki na jihohi don tattauna batun a faifai. Kana kuma a lokaci guda ya yi hannunka mai sanda ga masu neman ballewar, inda ya ce ba mutum ya kai kokensa ga wadansu kungiyoyi marasa kan gado ba.
Shugaba Muhammadu Buahri a cikin jawabin nasa, ya kara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a yankin Neja-Delta don samun dawwamanman zaman lafiya a yankin. “Muna da niyyar magance sahihan matsalolin al’ummomin yankin,” a cewarsa.
Haka kuma ya tabo batun rashin ayyukan yi a kasar, inda ya ce zai samar da ayyukan yi ga matasa marasa aiki kimanin dubu 10 a kowace jiha da ke fadin kasar. Shugaban ya ce zai yi hakan ne ta hanyar wani sabon shiri da Babban Bankin Najeriya (CBN) zai bullo da shi. Amma sai dai shugaban bai fadi tsawon lokacin da yake fatan cika alkawarin samar da ayyukan ba.
Bugu da kari, shugaban ya yaba da wa dakarun sojin Najeriya kan galabar da suke samu a kan mayakan Boko Haram. “Dole mu gode wa zakakuran sojojinmu kan yadda suka fatattaki ‘yan Boko Haram, suka samu nasara a kansu, kuma aka rage yawan hare-haren da ake kaiwa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.”
Daga nan ya ci gaba da cewa “Ba za mu yi kasa a gwiwa ba, domin an fara fadada aikin rundunar Lafiya Dole da take aiki a yankin na Arewa-maso- Gabashin Najeriya. Har ila yau ya gode wa makwabtan kasashe da sauran kasashen duniya game da taimakon da suke bai wa Najeriya a fagen yaki da ta’addanci.”
Haka zalika ya ce gwamnatinsa tana aiki ba dare, ba rana wajen ganin an ceto sauran ‘yan matan Chibok da sauran mutanen dake hannun mayakan Boko Haram. “Gwamnati za ta taimakawa dakarun kasar nan ba kawai a yaki da ta’addanci ba, har da matsalolin satar mutane don neman kudin fansa da fashi da makami da kuma rikicin makiyaya da manona,” in ji shi.
Game da batun tattalin arziki kuma, shugaban ya bayyana shirye-shiryen da gwamnatinsa ke yi wajen ganin Najeriya ta rage dogaro kacokan kan man fetur. Sannan ya bayyana irin taimakon da gwamnatinsa ke bayarwa a fannin aiki gona.
Daga nan ya tabo batun matsalar wutar lantarki, inda ya ce kasar ta na da burin samar da karfin Mega-Watt dubu 10 kafin nan da shekarar 2020 daga adadin dubu 7 da 100 da ake samarwa a yanzu. Haka kuma ya ce wata bakwai ke nan yanzu a jere hauhawar farashin kayayyaki ke ci gaba da raguwa a Najeriya.
Ya kuma tabo batun yadda darajar Naira ke cigaba da farfadowa idan aka kwatanta ta da dalar Amurka. Haka ma batun yadda kasar ke fitowa daga matsin tattalin arziki.
Game da batun cin hanci da rashawa kuma, ya ce a shirye yake ya ga bayan matsalar cin hanci da kabar rashawa, kamar dai yadda ya saba shan alwashin yin hakan a baya. Daga nan ya zayyana shirye-shireyen gwamnatinsa wajen magance matsalar.
Haka zalika Shugaba Muhammadu Buhari ya yaba wa Majalisar Dokoki ta Tarayya game da ayyukan kwamitocinta wadanda suke sanya ido kan yadda ake tafiyar da ayyukan gwamnati. Ya kuma bukace su da su yi dokokin magance cin hanci. A karshe ya bukaci daukacin al’ummar kasar da su tashi tsaye don yakar cin hanci ta hanyar kin ba da shi, da kuma karbarsa.