Najeriya ba za ta wargaje ba – Jonathan
Shugaba Goodluck Jonathan ya ce Najeriya ba za ta wargaje ba nan da shekara 100 masu zuwa, inda ’yan kasar za su yi bikin cika shekara 200 cikin yanayi mai kyau da walwala.Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a jawabinsa ga jama’ar kasa kan cikar kasar nan shekara 100.Ya ce: “Shekara 100 ba kwana 100 […]

Shugaba Goodluck Jonathan ya ce Najeriya ba za ta wargaje ba nan da shekara 100 masu zuwa, inda ’yan kasar za su yi bikin cika shekara 200 cikin yanayi mai kyau da walwala.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a jawabinsa ga jama’ar kasa kan cikar kasar nan shekara 100.
Ya ce: “Shekara 100 ba kwana 100 ba ne, a ranar 1 ga Janairun 1914 ne Turawan mulkin mallaka suka hade yankin Arewa da Kudu, inda daga baya suka zama Najeriya. Wannan hadewar ba wai kuskure ba ne, Allah ne Ya kaddara.”
Ya kara da cewa “Kowace kasa akwai matsalolin da suke ci mata tuwo a kwarya, ko Najeriya ta yi fama da Yakin Basasa, inda a yanzu wani bangare a kasar nan yake fama da ta’addanci, ina da yakinin Najeriya za ta sake tsallake dukkan matsalolin da suke ci mata tuwo a kwarya, ta zama kasa daya mai karfi.”
Shugaba Jonathan ya ce, idan aka yi la’akari da irin gwagwarmayar da aka yi da kuma yadda aka shawo kan matsalolin da suka dabaibaye Najeriya, “wannan ya sa nake da yakinin wadanda za su yi bikin cikar Najeriya shekara 200, za su yi cikin kwanciyar hankali da walwala. Za su yi wannan bikin ne idan har muka ci gaba da hada kanmu,”inji Jonathan.
Ya yaba wa mazan jiya da suka hada da Sa Abubukar Tafawa balewa da Sa Ahmadu Bello da Herbert Macauly da Dokta Nnamndi Azikwe da Cif Obafemi Awolowo da Alban Ikoku da sauransu bisa namijin kokarin da suka yi wajen nemo wa Najeriya ’yancin kai.
Ya ce, ya zama dole ya yaba wa sojoji bisa jajircewar da suka yi wajen tabbatar da Najeriya kasa daya, “Dole a yaba wa Janar Yakubu Gowon wanda bayan Yakin Basasa ya ce babu wanda ya yi nasara, babu kuma wanda aka samu nasara a kansa,” inji shi.
Ya ce tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Janar Abdulsalami Abubakar sun yi namijin kokari da suka mika mulki ga farar hula ba domin a tursasa musu ba.
Shugaban kasar ya yi Allah wadai da kashe ’yan makarantar Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Buni Yadi a Jihar Yobe da ’yan ta’adda suka yi a ranar Litini inda ya yi alkawarin za a shawo kan matsalar ta’addanci na dindindin.