Najeriya bayan shekara 58 da samun ‘yancin kai
Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Abin da ya sa na bude wannan makala da kalmomin nuna gadiya ga Allah (SWT), bai wuce duk da irin fadi-tashi da tashin-tashinar da kasar nan ta shiga da wadanda take ciki a yanzu ba, a zamanta na kasa da ta samu ’yancin kanta daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya a ranar […]
Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Abin da ya sa na bude wannan makala da kalmomin nuna gadiya ga Allah (SWT), bai wuce duk da irin fadi-tashi da tashin-tashinar da kasar nan ta shiga da wadanda take ciki a yanzu ba, a zamanta na kasa da ta samu ’yancin kanta daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya a ranar 1 ga Oktoban 1960 har yanzu tana nan a dunkule.
Kasar da har Yakin Basasa na shekara uku ta yi a tsakanin 1967 zuwa 1970, duk da haka da dadi ba dadi, har yanzu tana nan a zaman kasa daya. Sabanin wasu kasashe da muka samu ’yancin kai tare ko suka biyo bayanta da rigingimu da yake-yake suka raba su kamar Sudan, wadda har yanzu zaman lafiyar ya faskara.
Bayan godiya a kan wannan ni’ima da Allah Ya yi mana ta kasancewa kasa daya a tsawon wannan lokaci, wajibi ne in fara da ambaton shugabannin farko da suka shige gaba wajen samun ’yancin kai da fara dora kasar a kan harsashin tabbatar da zamanta kasa daya da kuma tunanin yadda ci gaba da hadin kan al’ummominsu zai tabbata. Wato mazan jiya irin su Sa Abubakar Tafawa Balewa da Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da Dokta Nnamdi Azikiwe da Cif Obafemi Awolowo da Cif Anthony Enohoro da Cif Herbert Macauly da Uwargida Femilayo Ransom-Kuti. A baya-baya akwai mutane irin su Malam Aminu Kano da sauransu.
Tabbas, tun a wancan lokaci zuwa yanzu kamar yadda na ambata, a zaman kasa daya ake, amma dai ana ta fama da rigingimun da suka game kasa masu kama da na addini da kabilanci da na siyasar ba namu yake mulki ba, don haka bari mu tada fitina, ta yadda mai mulkin zai rasa makamar tafiyar da gwamnatinsa, bare a ce ya yi wasu aikace-aikacen raya kasa da za su inganta rayuwar ’yan kasa har su ce madalla.
Sau tari idan irin wadannan rikice-rikice suka taso sai ka rantse cewa su za su kai ga raba kasar, ta yadda kowa zai kama gabansa, amma da sun lafa sai kuma ka ga kasar ta zauna daram, amma tabon wadancan fitinu suna nan tare da ’yan kasa musamman wadanda annobar ta shafa kai-tsaye.
Alal misali rikicin Boko Haram da ya dauko asali daga Jihar Borno a shiyyar Arewa maso Gabas, yau kusan shekara 10, sannu a hankali, ya mamaye jihohin shiyyar biyar da suka hada da Yobe da Bauchi da Adamawa da Gombe da Taraba. Kai sai da rikicin Boko Haram ya mamaye kusan jihohin kasar nan, kuma ya tsallaka zuwa makwabtan kasashe kamar Nijar da Chadi da Kamaru.
Amma yanzu alhamdulillahi! Don tun zuwan gwamnatin APC ta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kusan shekara hudu da suka gabata, askarawan kasar nan suke dakushe ta’addancin kungiyar ta Boko Haram. Samun saukin hakan ya sanya a bana Shugaba Buhari ya jagoranci kayataccen bikin zagayowar ranar ’yancin kai a dandalin Eagle Skuare da ke Abuja. Bikin da aka rabu da yi a bainar jama’a shekara takwas, bayan da wadansu ’yan ta’adda suka jefa bam a wajen taron a shekarar 2010, bam din da ya yi sanadiyar asarar rayuka da jikkata mutane da dama.
A irin wadannan rigingimu da kasar nan ta dade tana fama da su a wadannan shekaru, akwai rikicin kungiyar OPC ta ’yan kabilar Yarbawa. Akwai kuma ta ’yan kabilar Ibo masu fafutikar kafa kasar Biyafara wato IPOB. A shiyyar Kudu maso Kudu da ta kunshi jihohi masu arzikin man fetur, (Neja-Delta) an fuskanci ta’addancin tsagerun matasan yankin masu fasa bututun mai, fasa bututun da ke matukar kawo koma baya kan yawan danyen man da ake hakowa, wanda ke kan gaba wajen sama wa kasar nan kudaden shiga. Kai! ga ta’addancin garkuwa da mutane don neman kudin fansa da yanzu ya game kasar nan, kuma ya zama daya daga cikin manyan annoban da ke barazana ga zaman lafiya da karuwar arziki a yau daga yankin na Neja-Delta ya bullo.
Bayan wannan annoba da kusan kowace shiyya ta kasar nan take fama da ita, akwai kuma annobar fadan Fulani makiyaya da manoma da a iya cewa tsohon rikici ne na shekaru aru-aru da wasu jihohin Arewa suka dade suna fama da shi, amma a ’yan shekarun nan ya yi matukar kazancewa, sannan ya yadu a sassan kasa. Ga kuma fadace-fadacen kabilanci masu kama da na addini da suke ta karuwa a kullum. A gefe daya kuma ga matsalar satar shanu da kone garuruwa da uwa uba garkuwa da mutane, wanda duk tsautsayi ya fada masa za ta iya rutsawa da shi, sannan kusan komai mukamin mutum in ya je hannunsu sai an biya fansa zai samu ’yancin kansa. Wadansu ma a nan suke rasa rayukansu.
Wadanan matsaloli da ire-irensu sun addabi kasar nan kuma ana alakanta su kacokan a kan rashin adalcin shugabannin da suka biyo bayan zubin farko, bisa ga irin yadda sata da sama-da-fadi da dukiyoyin al’umma wato cin hanci da rashawa da ya zama ado, da ake cewa shi ne ummulhaba’isin dukan wadannan matsaloli, inda shugabanni suka mayar da dukiyoyin da za yi wa al’umma aikin raya kasa tamkar nasu. Alhamdulillah! Yanzu an samu gwamnatin da tun kafin ta zo kan karagar mulki, daya daga cikin abubuwan da ta yi alkawarin za ta yaka har da cin hanci da rasharawa. Wanda zuwa yanzu an fara gani a kasa. Don kuwa a zuwa yanzu gwamnatin tana samun irin wadannan shugabanni da laifin cin hanci da rashawa kuma tana daure su. Kamar tsofaffin gwamnonin jihohin Adamawa, Barista Bala Ngilari da na Taraba, Rabaran Jolly Nyame da na Filato, Mista Joshua Dariye.
Ana sa ran muddin hakan ya dore, to, kuwa kasar nan za ta kama turbar shiga cikin kasashe masu karfin tattalin arziki ta kowane fannin rayuwa, da zai ba da dama ’yan kasa su rika more rayuwarsu. Amma fa hakan ba zai tabbata ba sai ’yan kasar sun dage wajen zaben wakilai nagari masu rikon amana. Don haka samun nasarar ci gaban kasa mai dorewa zai dogara ne a kan talakawa tunda dai yanzu mulkin dimokuradiyya ake yi, ga kuma babban zaben kasa yana karatowa. Barkarmu da zagayowar wannan rana ta cikar Najeriya shekara 58 da samun ’yancin kai. Allah Ya maimaita mana cikin koshin lafiya da wadata, amin summa amin.