Najeriya ce kan gaba wajen kasuwancin sigari a Africa — CISLAC
Ƙungiyar ta buƙaci gwamnati da masu ruwa da tsaki su ɗauki gaɓaren hana yara ta’amalli da sigari a Najeriya.
Cibiyar Rajin Kyautata Ayyukan Majalisun Dokoki da Yaƙi da Rashawa (CISLAC), ta koka kan yadda matasa suka rungumi aƙidar shan taba sigari, duk da irin barazanar da ta ke da ita ga rayuwarsu.
Ƙungiyar ta bayyana damuwarta kan yadda Najeriya ta zama kan gaba wajen kasuwancin sigari a nahiyar Afirka.
CISLAC ta yi wannan koke ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a ranar Juma’a a Kano, don bikin Ranar Yaƙi da Shan Sigari ta Duniya ta 2024.
- Ainihin abin da Gwamnan Kano suka tattauna da Nuhu Ribadu
- Dalibai 30,000 sun yi nasarar rancen kudin karatu a kwana 6
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ware duk ranar 31 ga watan Mayun kowace shekara a matsayin ranar yaƙi da shan sigari ta duniya.
Ƙungiyar ta ce a bikin na wannan shekarar zai mayar da hankali ne wajen samar da hanyoyin da za a magance shan sigari a tsakina yara da manya a Najeriya.
A cewar CISLAC ta bakin shugabanta, Auwal Ibrahim Musa Rafsanjani, John CISLAC, ya bayyana cewar yadda kamfanonin da ke sarrafa sigari suna jan hankalin yara a kafafen sada zumunta musammam wajen tsara kwalin sigarin.
Ta yi nuna da yadda sabbin hanyoyin shan sigari suka fito irin su shisha da wasu na’ikan sigari da suka fito a baya-bayan.
Da ta bikin ranar, CISLAC ta yi kira da gwamnati da masu ruwa da tsaki tare da iyaye da su taka rawar wajen hana matasanmu na goge daga gurɓata tarbiyya a dalilin shan ta.
A cewarta gwamnati da sauran hukumomin da ke da alaƙa da rage illar sigari da su rage yaɗuwarta, don rage tasirin sauyin yanayi, gurɓatar muhalli da kuma tasirin tattalin arziƙi.