Najeriya ce kasa ta 10 a yawan ’yan Crypto a duniya – Rahoto
Wani kamfanin hada-hadar kudaden intanet, EMURGO Africa, ne ya bayyana haka
Wani kamfanin hada-hadar kudaden intanet mai suna EMURGO Africa, ya ce Najeriya ce kasa ta 10 da mutanenta suka fi ta’ammali da kudaden intanet wato crypto a duk fadin duniya.
Kamfanin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya ba Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Legas ranar Juma’a.
- Mahara sun kashe manoma uku a gonakinsu a Birnin Gwari
- Akwai barazanar harin ta’addanci da Sallah – DSS
Bayanin na kunshe ne a cikin wani rahotonsa mai taken: “Fasahar intanet zagaye na uku”.
Kamfanin ya ce rahoton nasa ya bayar da cikakkun bayanai a kan tasowa da kuma karbuwar fasahohin na intanet a nahiyar Afirka da yankin Gabas ta Tsakiya.
EMURGO Africa dai ya ce rahoton ya nuna matsayin Najeriya a kan yawan hada-hadar kudade ta intanet da kuma yadda take bunkasa cikin gaggawa.
“Hakan dai na nuna yadda fasahar take dada bunkasa a nahiyar Afirka. Wadannan alkaluman sun nuna yadda ’yan kasar ke ci gaba da rungumar harkar ka’in da na’in a fadin duniya,” in ji kamfanin.
Rahoton ya kuma nuna cewa fasahar gada-hadar kudaden ta karu da kaso 1.66 cikin 100 a 2022, idan an kwatanta da shekarar da ta gabace ta, da kuma jimillar kudaden da suka kai Dalar Amurka biliyan 91 a kasashe irin su Kenya da Afirka ta Kudu da kuma Najeriya.