Najeriya da Benin sun bude cibiyar hadin gwiwa ta hada-hadar kasuwanci

A ranar Talatar da ta gabata ce hada-hadar kasuwanci da harkokin shigi da fici tsakanin Najeriya da Jumhuriyar Benin suka tsaya cik, a lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaba Patrice Talon na Jumhuriyar Benin da Shugaban Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), Mista Jean-Claude Brou suka jagoranci bikin bude katafaren ginin hada-hadar kasuwanci […]

Najeriya da Benin sun bude cibiyar hadin gwiwa ta hada-hadar kasuwanci
Najeriya da Benin sun bude cibiyar hadin gwiwa ta hada-hadar kasuwanci

A ranar Talatar da ta gabata ce hada-hadar kasuwanci da harkokin shigi da fici tsakanin Najeriya da Jumhuriyar Benin suka tsaya cik, a lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaba Patrice Talon na Jumhuriyar Benin da Shugaban Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), Mista Jean-Claude Brou suka jagoranci bikin bude katafaren ginin hada-hadar kasuwanci da shigi da fici tsakanin Kasashen biyu masu makwabtaka da juna da ECOWAS ta gina a kan iyakar Seme.

Duk da yake Shugaba Buhari da mukarrabansa sun isa kan iyakar Seme ne a cikin Jirage masu saukar Ungulu a ranar, sai dai an tsaurara matakan tsaro ta fannin janye jami’an kwastam da jami’an shigi da fici da sojoji da ‘yan sanda a wurare daban-daban da suka saba yin zaman dirshan suna binciken masu shiga da fita a kan wannan babbar hanya da ta hade kasashen biyu. Kananan motocin tasi da ‘yan Okada da suka saba cunkusa buhunan shinkafa da wasu kaya ba su yi aiki a wannan rana ba.

Da yawa daga cikin direbobin motocin tasi da masu Okada da Aminiya ta zanta da su da aka sakaya sunansu, sun nuna damuwarsu da hana su yin aiki a wannan rana kamar yadda daya daga cikinsu ya ce, “ina matukar farin ciki da bude wannan cibiyar da Shugaba Buhari ya yi, amma ai wannan biki bai shafi ayyukanmu da muke fita tun da safe har dare domin abun da za mu ci tare da iyalinmu ba. Kamata ya yi su tsaurara matakan tsaro a daidai wuraren da ake yin bikin.”

Wani dan Okada cewa ya yi “tun farko ba a gaya mana za a dauki irin wannan matakin tsaro da ya takura mana ba sai kawai muka wayi gari da tilasta mana zaman gida ba tare da shiri ba.”

Aminiya ta yi kicibis da wata matar aure a cikin motar tasi da ta ce, “wannan bai hana ni yin kasuwanci tsakanin Najeriya da Benin ba, amma abun mamaki shi ne ya ya za a hana irin wadannan mutane yin aiki a kan wannan hanya alhali an sani cewa Shugaba Buhari ba zai gitta ta hanyar ba. Na so ace Shugaba Buhari ya biyo ta kan wannan hanya daga Legas zuwa Seme domin shi ma ya dandana kudar kwazazzabai da ramuka da muke fadawa cikinsu a kullu yaumin ba tare da gwamnati ta gyara ba.”

Cikin jawabinsa a wajen bikin, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce akwai bukatar gudanar da ayyukan gina mahadar hadin gwiwa ta kasa da kasa a kan iyakokin kasashen Afirka ta Yamma domin bunkasa harkokin kasuwancin kasashen. Ya ce, wannan katafaren ginin hadin gwiwa na hada-hadar kasuwanci da shigi da fici a kan iyakar Najeriya da Benin shi ne dandalin da ya fi ko’ina kai kawon jama’a, ba a Afirka ta yamma kadai ba har ma da kasashen Afirka baki daya. Ya jinjina wa takwaransa na kasar Benin, Shugaba Patrice a kan hobbasan da ta yi wajen ganin an kammala wannan aiki da goyon bayan Najeriya.

Shugaba Patrice Talon na Benin da Shugaban Kungiyar (ECOWAS) Mista Jean-Claude Brou da wakilin Kungiyar Gamayyar Turai (EU) da Jakadan Najeriya a Kasar Benin, Mista Kayode Emmanuel duka sun yi bayanai a kan hadin kan kasashen Afirka domin ci gaban al’ummarsu da bunkasar tattalin arzikinsu.

Shugaban Hukumar Kwastam na Kasa, Kanar Hameed Ali mai ritaya da Shugaban Hukumar Rundunar Shigi da Fici na Kasa, Babandede su ne suka jagaoranci takwarorinsu na kasashen Afirka ta Yamma zuwa wajen bikin. Shi kuwa mai masauki Kwanturola Muhammed Uba Garba na kan iyakar Seme shi ne ya jagoranci takwaransa na kasar Benin wajen tarbar manyan baki daga kasashen Afirka da dama.