Najeriya da Kamaru sun sha alwashin murkushe Boko HaramNajeriya da Kamaru sun sha alwashin murkushe Boko Haram
Gwamnatocin Najeriya da Kamaru sun yi alkawarin murkushe Boko Haram da tuttuge mayakanta daga kasashensu biyu da kuma yankin Tafkin Chadi inda suka nuna gamsuwa da nasarar da aka samu a baya-bayan nan a yakin da ake yi da mayakan kaungiyar Boko Haram.Wannan bayani yana kunshe a cikin sanarwar bayan taron da aka fitar a […]
PIC PRESIDENT MUHAMMADU BUHARI (R) ADDRESSING A JOINT PRESS CONFERENCE WITH THE VISITING PRESIDENT PAUL BIYA OF CAMEROUN AFTER A BILATERAL MEETING IN ABUJA ON WEDNESDAY (4/5/16) 4/5/2016/ICE/NAN

Gwamnatocin Najeriya da Kamaru sun yi alkawarin murkushe Boko Haram da tuttuge mayakanta daga kasashensu biyu da kuma yankin Tafkin Chadi inda suka nuna gamsuwa da nasarar da aka samu a baya-bayan nan a yakin da ake yi da mayakan kaungiyar Boko Haram.
Wannan bayani yana kunshe a cikin sanarwar bayan taron da aka fitar a shekaranjiya Laraba a tsakanin kasashen biyu a karshen ziyarar da Shugaban kasar Kamaru Mista Paul Biya ya kawo wa takwaransa na Najeriya Shugaba Muhammadu Buhari a Abuja.
Minisatan Harkokin Wajen Najeriya Mista Geofrey Onyeama da takwaransa na Kamaru Mista Mbella Mbella suka bayyana haka lokacin da suka karanta takardar bayan taron a Abuja.
Sun ce kasashen biyu suna Allah wadai da miyagun ayyukan da kungiyar take aikatawa a kasashen gabar Tafkin Chadi, inda suka yaba wa sojojin hadin gwiwa na kasashen yankin (MNJTF) kan kokarin da suke yin a kawo karshen aika-aikar kungiyar ta’addar.
Sun kara da cewa Shugaba Buhari da Shugaba Biya sun sake nanata kudirinsu na ci gaba da bayar da goyon baya ga sojin hadin gwiwa na JMNTF har sai sun murkushe ’yan ta’addan baki daya.
Sai suka bayyana bukatar kafa wata kotun musamman domin hukunta mayakan Boko Haram da yadda za a mayar da su kasashensu na asali kamar yadda dokokin kasashen duniya suka tanada.
kasashen biyu sun kuma amince a koma fagen sake shata kan iyakokin kasashen biyu sakamakon dawowar zaman lafiya a yankin, inda suka ce kwararru daga kasashen biyu da kuma hukumomin hadin gwiwa na Najeriya da Kamaru su hanzarta komawa don shata kan iyakokin nan ba da jimawa ba.
Sanarwar ta ce shugabannin biyu sun amince su karfafa hukumar hadin gwiwa na Najeriya da Kamaru ta hanyar kara mata karfi ta tsara tare da daidaitawa da aiwatar da dukkan yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka sanya hannu a kai ta yin amfani da samfurin Hukumar Hadin Gwiwa ta Najeriya da Nijar.
Minista Onyeama wanda ya karanto takardar bayan taron cikin harshen Ingilishi ya ce ziyarar ta Shugaba Biya ta dada karfafa “ingantacciyar dangantakar tarihi da abokantaka da ’yan uwantaka da kyakkyawar makabtaka” da ke tsakanin kasashen biyu.
Najeriya da Kamaru sun kuma sanya hannu a kan yarjeniyoyi daban-daban da suka shafi tattalin arziki da zamantakewa.