Najeriya da Pakistan sun yi taron bunkasa cinikin magunguna

An gudanar  da  taron yini  biyu  tsakanin  masu  sarrafa  magunguna  na Najeriya da  takwarorinsu na kasar  Pakistan a birnin Ikko  domin samar da hanyoyin bunkasa  harkokin samar da  magunguna  a Najeriya, cikin sauki  kuma  ingantattu.Da yake jawabin wajen taron,  daya daga  cikin  shugabannin taron, Alhaji Ibrahim Ahmed Yakasai  ya ce an zabi kasar  Pakistan ne […]

Najeriya da Pakistan sun yi taron bunkasa cinikin magunguna
Najeriya da Pakistan sun yi taron bunkasa cinikin magunguna

An gudanar  da  taron yini  biyu  tsakanin  masu  sarrafa  magunguna  na Najeriya da  takwarorinsu na kasar  Pakistan a birnin Ikko  domin samar da hanyoyin bunkasa  harkokin samar da  magunguna  a Najeriya, cikin sauki  kuma  ingantattu.
Da yake jawabin wajen taron,  daya daga  cikin  shugabannin taron, Alhaji Ibrahim Ahmed Yakasai  ya ce an zabi kasar  Pakistan ne domin yin wannan hulda saboda  tana daya  daga  cikin kasashen duniya  da ke da  kwarewa  wajen sarrafa magunguna, musammam a yankinsu na Asiya, kana suna da yanayi irin na Najeriya.
Alhaji Yakasai ya ce yanzu haka Najeriya da kasar Pakistan suna kasuwancin da yake da adadin Dala miliyan 100, wanda ganin ya yi kadan ya sa aka shirya taron  na yini biyu domin a kara  shi, musamman ta hanyar sarrafa magunguna.
Ya ce wannan taron shi ne harsashin matakin habako da masana’antun magunguna na gida  ta  yadda wadanda  suka  durkushe  za su samu  abokan hulda da  za su tado su  kuma ana sa ran wannan taron ya samar da karin aikin yi ga ’yan Najeriya.
Da kuma ya tabo  batun tsaro,  musammam a kan yadda ba za su fada mugun hannu ba, sai Alhaji Ibrahim ya ce sun cimma matsaya  game da  wannan.  Ya ce don  haka ne ma ya sa   gwamnati  ta kawo jami’an tsaro  cikin batun, musammam masu  nasaba  da  shiga da ficin kayayyaki  da mutane, tare da hukumomin da ke da hannu  wajen  ingancin abinci da magunguna da kuma duk  wani  mai ruwa  da tsaki  a harkar tsaron  abinci da kaya da mutane.
Da wakilin Aminiya ya tambayi daya daga cikin mahalarta taron, Malam Ahmed Salim abin da ya ba shi kwarin gwiwar zuwa, sai ya ce, “Najeriya kasa ce da ke da dimbin albarka, kana tana da wadatacciyar kasuwa da wajen sarrafa duk abin da mutum ke so, kuma ba zai yi da-na-sani ba”.
Ana sa ran samun masu sarrafa magunguna a nan cikin gida da kuma can kasar Pakistan din, kuma suna da damar shigowa da su nan Najeriya.