Najeriya da Sudan samma kal
Tun daga lokacin da aka tsaga kasar Sudan gida biyu a watan Yulin shekarar 2011 hankulan jama’ar kasashen biyu ba su kwanta lami lafiya ba, haka nan kuma ba su warware daga matsalolin yakin basasar da aka yi shekaru 25 tun kafin a kirkiro wata sabuwar kasar da yanzu ake kira Sudan ta Kudu ba. […]
Tun daga lokacin da aka tsaga kasar Sudan gida biyu a watan Yulin shekarar 2011 hankulan jama’ar kasashen biyu ba su kwanta lami lafiya ba, haka nan kuma ba su warware daga matsalolin yakin basasar da aka yi shekaru 25 tun kafin a kirkiro wata sabuwar kasar da yanzu ake kira Sudan ta Kudu ba. Babban abin da ya kai ga haifar da ita kuwa shi ne dimbin arzikin man fetur da ya tsole wa Turawan kasashen Yammacin Turai idanu, wadanda kasar Amurka ta yi ta taimakawa ta hanyar haddasa bambance-bambancen addini don farraka kawunan jama’ar kasar ta yadda za a fi su cin gajiyar arzikin man da aka gano a yankin kudancin kasar.
Ta haka ne Turawan da ke dasawa da shugabannin Arewacin kasar, wadanda yawancinsu Musulmi ne, suka zuga su don yin aiki da tsarin Shari’ar Musulunci kamar yadda addininsu ya bukace su da yi. Bayan sun amince da haka, sun kuma dauki matakan karfafa aiki da shari’ar, sai Turawan suka kuma koma wajen Kiristocin da suka yi katutu a yankin Kudancin kasar, suka hore musu kunnuwa don kada su yarda a yi aiki da shari’ar Musulunci a kasar domin hakan wani mataki ne na tursasa su bin tafarkin wani addini dabam da nasu.
A sakamakon haka ne bakar gaba ta ruru tsakanin Musulmin da suke da rinjaye a Arewacin kasar da kuma Kiristocin da suka yi kaka-gida a Kudanci, har sai da ta kai an yi kazamin yakin basasar da ya tilasta raba kasar don an dauka haka ne kawai mafita daga matsalar da rikicin addinin ya haddasa. To ko da aka yi hakan tsuguni-tashi ba ta kare ba, hankulan jama’ar Sudan ta Kudu ba su kwanta ba, Turawan da suka yi sanadiyyar ballewar kasar daga Sudan ba su samu biyan bukatunsu ba na kwasar garabasar dimbin man da suka kallafa ransu akai yadda suka so, saboda tsananin hadamar da ta rarraba kawunansu.
Cikin dan kankanen lokaci sai ga shi nan kasashen Yammacin Turai, wadanda suka yi ruwa da tsaki wajen rura fitintinun da suka jawo rabewar kasar Sudan, sun kasa daidaita sahunsu don su ji dadin tatsar sabuwar kasar a tsanake, su kuma hana jama’ar Sudan ta Kudu cin sabuwar duniyarsu su da tsinke. Hakan kuma ya sa kowace kasar nahiyar Turai da nata jan-gwarzon cikin shugabannin da take ganin shi ne zai taimaka mata shan arzikin man fiye da takwarorinta, wadanda su ma sun yi hakilo wajen daurewa wanda suke so gindi don ya danki ragamar mulkin kasar, ya kuma buda masu hanyar tatike arzikin kasarsa. Ilai kuwa sai ga shi nan bayan ‘yan shekaru biyu da kafuwar kasar Sudan ta Kudu an haifar da rashin jituwar da ta sanya kataniya tsakanin shugaba mai ci yanzu, Mista Sylba Kiir da kuma tsohon mataimakinsa, Riek Macher, sakamakon sabanin ra’ayi game da biye manufofin Turawa na dabarun hakar arzikin mai da kuma hanyoyin da za a bi a fitar da shi zuwa kasashensu.
Dambarwar da Turawa suka yi ta yi don mallakar arzikin man ya haddasa mummunar gabar kabilanci tsakanin mabiyan Shugaba Sylba Kiir, ‘yan kabilar Dinka da kuma ta tsohon mataimakinsa, Riek Macher, wato ‘yan kabilar Nuer, kuma hakan ya jawo kataniyar da ta sa Shugaba Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa da kokarin hambarar da mulkinsa, kuma a sakamakon haka mummunar tashin hankali ya barke a kasar, har ana tsoron hakan na iya zamewa gagarumin yakin basasa a kasar. Turawa ne dai suka haddasa wannan matsalar domin wasunsu na son a hambarar da gwamnatin Kiir, wanda suke ganin ya fi yi da abokan hamayyarsu fiye da su, kuma idan suka maye makwafinsa da mataimakinsa sai yadda suka ga dama za su juya shi.
Ta ko ina ka duba, biri ya yi kama da mutum, kamar yadda za a iya cewa matsalolin kasar Sudan sun zo daidai da wadanda suka dade da wanzuwa a kasar nan. Arzikin man fetur ya zame wa Najeriya masifa maimakon alheri, kuma hakan ya haddasa yakin basasar da ya janyo asarar dimbin rayuka, daga bisani kuma ya kasance hujjar raba kan jama’ar kasar nan bisa akidar kabilanci. Haka nan an yin amfani da addini kamar yadda aka yi a kasar Sudan, aka tayar da gagarumar fitina kan Shari’ar Musulunci, abin da ya kara rarraba hadin kan Musulmin kasar da kuma haddasa fitintinun da suke ba Turawa damar karkata akalar shugabannin Najeriya yadda suke so. Rikicin Sudan babban darasi ne ga ‘yan Najeriya, sun kuma kasa fahimtar haka balle su tsira daga wannan sharrin. A kullum wadannan matsalolin kara kamari suke yi, kuma babu wadanda suka fi kwaruwa game da haka kamar al’ummomin Arewar da aka rigaya aka yi amfani da addini don shiga tsakaninsu, sa’annan kuma rashin jituwar da ke kara raunana igiyar dangantaka da zamantakewarsu.
A wasu garuruwan ma har ta kai Kiristoci da Musulmi ba su gwamatsuwa wuri guda. A wasu jihohin ba a darjanta mabiya wani addini, ba a kuma yin wasu mu’amala da su. Kai! Har ma ta kai gwamnatin dimokuradiyya, wacce talakawa suka taru, suka zaba, ta koma hannun wasu ‘yan tsirarun da suke gara ta bisa tafarkin wani addini. Kaico!