Najeriya: Ga koshi ga kwanan yunwa (2))

A ranar Lahadin wannan makon ne Ofishin kididdiga na Najeriya, (watau National Bureau of Statistics a Turance) ya hakikance cewa Najeriya ce yanzu kasar da tattalin arzikinta ya dara na kowace kasa a nahiyar Afirka, kuma ita ce kasa ta ashirin da shida cikin jerin hamshakan kasashen duniya. Ofishin kididdigar ya ce hakan kuwa ya […]

Najeriya: Ga koshi ga kwanan yunwa (2))
Najeriya: Ga koshi ga kwanan yunwa (2))

A ranar Lahadin wannan makon ne Ofishin kididdiga na Najeriya, (watau National Bureau of Statistics a Turance) ya hakikance cewa Najeriya ce yanzu kasar da tattalin arzikinta ya dara na kowace kasa a nahiyar Afirka, kuma ita ce kasa ta ashirin da shida cikin jerin hamshakan kasashen duniya. Ofishin kididdigar ya ce hakan kuwa ya faru ne dangane da habakar  abubuwan da kasar ke samarwa, wadanda kuma ake fitarwa kasashen ketare don sayarwa ana samun kudaden musanya da kuma harajin da suke biya. Ta haka ne ake gane karfin arzikin kasashen duniya. To amma fa wajibi ne a kididdige wadannan al’amura bayan ’yan shekaru kamar biyar zuwa bakwai, amma rabon da a yi  wani abu makamancin haka tun a shekarar 1990.
Amma sai dai ofishin kididdigar ya ce zunzuruntun arzikin da ake samarwa a kasar a shekarun baya  ba su hada  da sabbin hanyoyin samar da kudade da ba a fara amfani da su ba a shekarun baya, kamar su fina-finan wasanni da na wake-wake da ake samarwa a nan cikin gida da kuma sabbin kamfanonin wayoyin hannu da suka zame ruwan dare, gidan kowa da akwai su, amma a yanzu da aka hada da su wajen kididdigar arzikin Najeriya ya kai Naira tiriliyan tamanin da digo uku (N80.trn -kwatankwacin Dalar Amurka billiyan 510). Abin da haka ke nufi shi ne arzikin da Najeriya ke samarwa a gida ya kai abin da daukacin gwamnatin tarayya da na jihohi za su yi kusan shekaru ashirin suna batarwa, idan aka yi la’akari da kasafin kudadensu na shekara-shekara da suke karkashewa. Idan kuma aka dubi abin da aka samu shekaru ashirin da suka shude, sai a taras adadin da aka kididdige a bana ya nunka na wancan lokacin nunkin-banunki. Ta haka ne aka gano cewa Najeriya ce kasa mafi karfin arziki a nahiyar Afirka, har ma ta dara kasar Afirka ta Kudu dangane da haka.  
To amma duk  da cewa kasar Afirka ta Kudu  na fama da matsalolin da ke haddasa tsumburewar tattalin arziki, kamar rashin tabukawar masana’antunta don samar da kayayyakin da za a sayar a wasu kasashe da  rashin aikin yi da ya yi katutu a kasar, kamfanonin kasarta na tabukawa wajen habaka tattalin arzikin Najeriya ta fannonin saye da sayarwa da kuma harkokin sadarwa, musamman a harkar wayoyin hannu irin su bodacom ke taimakawa. Ta ko’ina aka duba, sai a fahimci cewa kamfanonin kasashen Afirka ta Kudu na taimakawa matuka wajen habaka arzikin nahiyar Afirka fiye da kowace kasa.
To amma  duk da cewa wai Najeriya ta yi wa tsararrakinta na nahiyar Afirka fintinkau a wannan fannin, amma babu yadda za a iya kwatanta ci gaba da habakar tattalin arzikinta da na Afirka ta Kudu, domin kuwa yawan rashin aikin yi bai tsananta a can ba kamar a Najeriya, kuma masana’antun kasar na nan na ci gaba da ayyukansu gadan-gadan, ba su durkushe da siradansu ba kamar yadda na Najeriya suka ruguje baki daya. A Najeriya karfin wutar lantarki kimanin Megawatt 3,000 da ake samarwa fiye da shekaru goma sha  biyar, duk da dubban miliyoyin Dalolin da aka narkar, kuma karancin wutar ya janyo karayar arzikin kamfanoni da yawa, ba kamar a kasar Afirka ta Kudu ba, inda karfin wutar lantarki na Megawatt fiye da 40,000 ke bunkasa harkokin masana’antu da kasuwanci.  Baicin haka nan kuma ’yan kasar Afirka ta Kudu da masana’antunta ba su wasa da biyan haraji, kuma hakan na kara yawan arzikin da ke habaka arzikin kasar. Baicin haka nan kuma masana tattalin arzikin kasashen duniya sun tabatar da cewa kaskantaccen talakan Najeriya na dogara ne kan Dala 1.25 (kasa da Naira 200 a kullum) alhali kuwa takwaransa na kasar Afirka ta Kudu kan dogara ne bisa Dala 6.75   (kwatankwacin Naira 1,100 a kullum).
Shi ya sa wasu ’yan Najeriya da suka san yadda yanayin kasashen biyu ke kasancewa, suke cewa ofishin kididdigar Najeriya dai ya bi son ransa ne, ya fitar da wannan bayanin a daidai lokacin da Babban Bankin Duniya ya fitar da ingantaccen rahoton da ke nuna cewa Najeriya ce kasa ta biyu daga cikin guda biyar a duniya da talakawan cikinta suka dara na ko’ina tagayyara saboda tsabar talauci. Kuma ko ba a fada ba, an san da haka, domin ga shi nan duk da tiriliyoyin Naira da ake kasaftawa, ana batarwa a kowace shekara, talakan Najeriya bai amfana da ko karfanfana, ya zame tamkar matsiyacin da ake dulmuyawa a tandun mai, haka nan yake fitowa fari fat, ba alamun maiko a jikinsa. Idan da gwamnatin tarayya na amfani da dimbin dukiyar da take samu don amfanin jama’ar kasar nan, ai da talaka ya daina kwanan yunwa da rashin aikin yi ko samun muhallin da zai shimfida hakarkarinsa bayan dawainiyar neman abinci.
Amma da yake don siyasa aka kirkiri wannan bayani, talaka bai san da haka ba, domin ba ya gani a kasa. dimbin arzikin da ake samu bai sa talaka na amfana da asibitocin da suka zame fanko ba; ’ya’yansa ba su samun ilimi mai amfani; babu sauran kayayyakin more gardin rayuwa da za su tabbatar masa cewa ba zaman jiran mutuwa kadai yake ba a Najeriya, kuma komai wayyon-Allah da yake yi, haka nan mahukunta za su yi ta kankararsa, har sai ya gwammace mutuwa da rayuwa cikin kunci da wulakanci.