Najeriya: har yanzu tsinuwar na nan? (3)
Saboda haka muna iya cewa munafincin mutanen waje shi ya kawo barakar da ta kunno kai daga 1966, wadda ita ta kara wagewa har zuwa 1967 da kuma tashin-tashinar tsakanin 1968 zuwa 1970, wanda kuma tabon wannan tashin-rashina shi ya haifar da lalacewar da Najeriya ta samu kanta a ciki. Idan muka ce kila tsakanin […]
Saboda haka muna iya cewa munafincin mutanen waje shi ya kawo barakar da ta kunno kai daga 1966, wadda ita ta kara wagewa har zuwa 1967 da kuma tashin-tashinar tsakanin 1968 zuwa 1970, wanda kuma tabon wannan tashin-rashina shi ya haifar da lalacewar da Najeriya ta samu kanta a ciki. Idan muka ce kila tsakanin shekarun 1967 zuwa 1970 ne Najeriya ta fara Allah-Wadai da ‘ya’yanta da suka fandare, suka yaki juna, suka warwatsa zumunci da son juna tsakanin ‘ya’ya da jikoki ba za mu yi kuskure ba. Domin kuwa a daidai wannan lokaci ne aka gane cewa ashe Najeriyar daya ce, amma wai kowa ya san gidan ubansa. Daga wannan lokaci kuwa bakin Najeriya ya hau kan ‘ya’yanta, da alama kuma daga wannan lokaci ne ‘ya’yan suka fara lalacewa da balbalcewa. |
Mu dubi abin da ya faru daga shekarun 1970 zuwa 1983. A daidai wannan lokaci ne za a ce Najeriya ta samu dukkan arzikin da take tinkaho da shi, shi ya sa wasu daga cikin ‘ya’yan nata suke fadar matsalar Najeriya a lokacin ba ta rashin tarin dukiya ko arziki ba ne, abin da za a yi da tarin dukiyar ko arzikin shi ne matsala. Daga jin irin wadannan kalamai daga bakunan wasu daga ciki ‘ya’yan nata, za mu fahimci cewa ko dai ‘ya’yan sun fara sonsomin hauka ko kuma dadin arzikin Najeriya ya bibiye musu kai, ba su gane gabas, bare yamma. Wannan wuji-wuji ina gabas da aka yi wa wasu daga cikin ‘ya’yan Najeriya ya sa suka yi watsi da uwar tasu Najeriya.
A maimakon ‘ya’yan su samar da abubuwan da za su faranta wa uwar tasu rai, sai suka shiga facaka da dukiyarta, su ne shirya bukukuwan al’adu na ba gaira ba dalili da giggina otel-otel na alfarmar da bai agaza wa Najeriya ba. Sa’annan ga bayar da kwangilar ayyuka da ba su da wani tasiri ga ci gaban kasar. Ina kuma jin ganin irin yadda ‘ya’yan nata suka kasance a lokacin ya sa Najeriya ta fara kuka da shessheka, ga tsufa ya kamata, amma ‘ya’yan nata suka kasance tamkar Wowwo dan Malam, ka ki halin Malam, rago da wutsiyar kare! Ina kuma jin daga lokacin ta shiga fitowa fili ta fara tsine wa ‘ya’yan nata, kuma daga lokacin ne al’amurra suka fara dagulewa.
Shi ya sa daga shekarar 1983 aka fara ganin alamun ‘yan Najeriya na cikin tsaka mai wuya. Ba kuma wani abu ya jawo haka ba sai ganin Najeriya ta dai tsine wa wasu daga cikin ‘ya’yan nata, saboda haka wahala da damuwa da kunci sun fara zama ruwan dare, duk da cewa an samu wasu da suka nemi su dinka wa Najeriya sabuwar riga ko zane, amma ba a bar su suka kai labari ba. Haka al’amurra suka ci gaba da gudana har zuwa 1985. Shi ya sa aka shiga watangaririya da Najeriya. Wannan mai karfin hali ya kashe wancan da ya ki goya masa baya. Wancan dakaren daga cikin ‘ya’ya ya sa bindiga ya harbe wancan. Wancan ya boye a wata kwana yana jira wani ya leko, shi kuma ya buge shi. Haka aka yi ta fama tun daga 1985 har zuwa 1999. Ba rana ko wata da ‘ya’yan nan suka taimaka wa Najeriya, in ba cin mutuncin ta ba. In ta yi asusu ta tara dukiyar, su bi su sace! In ta matsa su yi ayyukan ci gaba don ciyar da ita gaba, su fara zagi da watsar mata da duk wani tanadi da ta yi domin ‘yan baya. Tsinannun ‘ya’yan nata ne suka bi duk harkokin da ta tanada na ilmantar da wasu ‘ya’yan suka lalata. Makarantun da ta tsara domin talakawa da marasa galihu, suka fancakalar da su, suka gina nasu da na ‘ya’yansu, kowa sai tsuwa da ihu. A irin wannan yanayi me zai hana Najeriya ta ci gaba da tsine wa irin wadannan ‘ya’yan nata?
Mu tsaya mu yi wa kanmu hisabi. Shin idan Najeriya ba ta tsine wa ‘ya’yanta ba ne, me ya sa kullum abin da ke tashe a cikin kasar shi ne wayyo Allah da ni-‘ya-su. Me ya sa ‘ya’yanta, musamman shugabanni, a kowane mataki sun kasance makafi, ba su gani balle su agaza wajen ciyar da ita gaba. Ba abin da suka gwanance kai face halin dan bera? Abin ban haushin shi ne, in sun sace, ba su san su tsaya su ci da ‘yan uwa ba, sai dai su kwashe su je su kimshe a wata kasar, don mugunta. Idan ba wadanda aka tsine wa ba, wa ke da wannan dabi’ar?
Mu dubi masu kudi da tarin dukiyar da ke cikin kasar nan, sun tara, sun sake tarawa, wasu daga cikin su, su ne suka fi kowa tara dukiya a nahiyar Afirka, amma in ka tambaya wace gudunmawa suka bayar wajen raya gida Najeriya, da wuya ka iya kididdigewa. Su ne da manyan-manya da kuma tafka-tafkan gidaje da jiragen sama da shiga dibga-dibgan motoci da banzatar da duk wani abu da zai taimaki jama’a, duk da tarin dukiyar, amma makwabta da ‘yan uwa na kusa da su, na cikin tasku. Shi ya sa kullum suke cikin zullumi da tashin hankali. Idan uwarsu Najeriya ba tsine musu ta yi ba, ina dalilin aukuwar haka?
Wasu daga cikin ‘ya’yan nata, wai su ne malamai da fasto-fasto, amma addu’ar da suke faman yi kullum iyakarta a cikin tafin hannunsu. Ba komi ya jawo haka ba, sai ganin bakin da ke furta addu’ar, bai tafiya tattare da kyakkyawar zuciya. Shi ya sa suna neman sauki daga Allah, shi kuwa Allah na kara azabtar da su da sauran al’umma. Ba wani abu da ya jawo haka ba, sai alamun cewa lallai mahaifiyarsu ta yi musu baki, dole suke lalacewa da balbalcewa.
Za Mu Ci Gaba