Najeriya ina muka dosa?

Idan kana bibiyar al’amurran kasar nan a kafafen watsa labarai na rediyo da talabijin da intane a kullum masu fashin baki a kan al’amurran yau da kullum kukan da suke yi shi ne turbar da kasar nan ta dosa a yau ba zai haifar da da mai ido ba. Idan ta haifa, to shaidani za […]

Najeriya ina muka dosa?

Shugaba Goodluck JonathanIdan kana bibiyar al’amurran kasar nan a kafafen watsa labarai na rediyo da talabijin da intane a kullum masu fashin baki a kan al’amurran yau da kullum kukan da suke yi shi ne turbar da kasar nan ta dosa a yau ba zai haifar da da mai ido ba. Idan ta haifa, to shaidani za ta haifa wanda zai zama fitina ga al’umma a dawo ana da na sanin haihuwarsa. Wanda idan abin ya yi kamari, zai iya zama ajalin iyayen da suka yi sanadiyyar zuwansa duniya kamar yadda ya faru da Malam Shehu mahaifin Abubakar a cikin littafin Jiki Magayi, “An African Night Entertainment”.
A yau, wasoso da watanda da dukiyar kasa sun zama ruwan dare a tsakanin manyan jami’an wannan gwamnati, inda a kwanan nan Ministar Sufurin Jiragen Sama Misis Stella Oduah ta yiwo cefanen motoci masu sulke na Naira miliyan 255 da sunan kare lafiyarta daga barazanar da take fuskanta, kuma gwamnati ta yi gum a kan batun, saboda tana daga cikin shafaffu da mai masu juya akalar Shugaban kasa.
Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da malaman jami’o’in kasar nan suka ta samma shiga wata na hudu suna yajin aiki a kan a kara kason kudin inganta ilimi a makaratun kasar nan domin amfanin miliyoyin daliban kasar nan, amma gwamnati ta ki kallonsu da idon basira bare ta share hawayensu a inganta ilimin.
Ga Maina da ake zargi ya yi sama da fadi da makudan kudin da ya kwato daga barayin fensho, shi ma shiru kake ji, kamar malam ya ci shirwa. Babu wani katabus daga gwamnatin kasar nan, sai ma
tsaro na musamman da ririta shi da gwamnati ke yi. Ban da badakalar binciken su dan majalisa Faruk Lawan da batun ya koma wasan kwaikwayo, sai rahoton kwamitin Nuhu Ribadu da aka yi a sha ruwan tsuntsaye da shi, wanda hakan ke nuna wannan gwamnati dabaibaye take da cin hanci da rashawa da rashin tabbas na makamar dafawa.
Shin a haka take tunanin sake shugabantar mutanen kasarta? Ai ko a duniyar dabobbi, idan zaki ya ce
zai tafiyar da dabbobi irin haka, to labudda sauran dabbobi irin su giwa da damisa da kura ba za su amince da irin wannan jagoranci ba, kuma za su yi iya yinsu su ceto gandunsu daga rugujewa a hannun makahon jagora.
Ga wani abu da ta tsiro da shi sabo da rana tsaka mai suna “Taron kasa,” wanda shi ma hasashe na nuna ba zai haifar da mai ido ba! Musamman a yankin Arewa da rikicin Boko Haram ya tagayyara. Hakika
yadda al’amurra ke ci gaba da lalacewa a kasar nan da rashin katabus na wannan gwamnati, ya jefa mutane da dama cikin tunanin shin ina makomar kasar nan ke dosa a haka?
A kullum idan al’amurra sun faru ana kokarin kafa kwamitoci amma abin da suka kawo ba a aiki da shi,
haka ake asarar kudi a banza na kafa kwamitin. Shi ma taron kasar, kusan asarar kudin ne za a yi su tafi a banza.
Sannan hukumomin tsaro sun zama ’yan amshin shata, sai yadda gwamnati ta yi da su, ana neman a maida kasar tamkar zamanin mulkin soja. Duk mai adawa da gwamnati sai an san irin bi-ta-da-kullin da aka yi don karya shi ko ya bi. Al’amuran tsaro sai kara tabarbarewa suke yi musamman a jihohin Borno da Yobe, babu wani ci gaba da aka samu ban da yawaitar asarar rayuka a kullum, duk da dokar ta-baci da aka kakaba musu, abin ya zama gwanda jiya da yau. Haka abin yake a kudancin kasar nan wajen sace mutane da yin garkuwa da su da safarar miyagun kwayoyi, ga ’yan ta’addar Neja-Delta da ke cin karensu ba babbaka wajen satar mai.
A bangaren kiwon lafiya kuwa yadda ake asarar rayuka a kullum, sai dai a yi shiru. Batun yadda talauci ya yi kaka-gida a tsakanin al’ummar kasar nan kuwa duk da dimbin arzikin da ke akwai, abin ya wuce tunanin mai hankali.
Anya a tafiyar da kasar nan ke yi za ta gadar mana da alheri kuwa? A gaskiya lamarin da kamar wuya, idan ba an canja akalarta ba, domin hanyar da ta tunkara ba mai bullewa ba ce.
Ahmad A. Daura
MTN Daura, Jihar Katsina.
08032320871

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50