Najeriya na asarar Dala biliyan 1.1 a duk shekara saboda zazzabin cizon sauro

Najeriya na yin asarar sama da dala biliyan 1.1 a duk shekara sakamakon zazzabin cizon sauro

Najeriya na asarar Dala biliyan 1.1 a duk shekara saboda zazzabin cizon sauro

Sauro

Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na yin asarar sama da dala biliyan 1.1 a duk shekara sakamakon zazzabin cizon sauro, wanda ke yin tasiri sosai ga tattalin arzikin kasa.

Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate ne ya bayyana hakan a yayin taron kaddamar da shirin kawar da zazzabin cizon sauro a Najeriya (AMEN) a Abuja.

Farfesa Pate ya bayyana cutar zazzabin cizon sauro ba kawai matsalar lafiya ba ce, matsala ce ta tattalin arziki da ci gaban da ya kamata a magance cikin gaggawa.

Ya kara da cewa Najeriya ce ke da kashi 27% na masu fama da cutar zazzabin cizon sauro a duniya, da kuma kashi 31% na mace-macen da ke da nasaba da zazzabin cizon sauro a duniya.

Ya ce a shekarar 2022 kadai, sama da yara 180,000 ’yan kasa da shekara biyar a Najeriya ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro, bala’in da za a iya karewa.

Ministan ya ce kaddamar da kwamitin ba da shawara wani shiri ne na gwamnati don magance matsalolin da suka danganci cutar da illarta ga cigaban lafiya da tattalin arziki.

Kotu ta jingine hukunci a shari’ar kuɗin ƙananan hukumomin Kano

Isra’ila ta tsagaita wuta a Lebanon

Za a yi sallar roƙon ruwa a Saudiyya

Kotun ta bai wa EFCC umarnin tsare Yahaya Bello