Najeriya na asarar sama da Dala biliyan 2 duk shekara akan safarar jakuna – DSPMEAN

Kungiyar DSPMEAN ta soki shirin kafa doka da Majalisar Wakilai ke shirin yi   Kungiyar masu sarrafa fatar jakuna da fitar da ita zuwa waje ta Najeriya (DSPMEAN), ta soki shirin kafa dokar dakatar da fede fatar jaki da sayar da ita a kasashen waje ko kuma dakatar da yanka jakunan. An kai matakin karatu […]

Najeriya na asarar sama da Dala biliyan 2 duk shekara akan safarar jakuna – DSPMEAN

Jakuna

  • Kungiyar DSPMEAN ta soki shirin kafa doka da Majalisar Wakilai ke shirin yi

 

Kungiyar masu sarrafa fatar jakuna da fitar da ita zuwa waje ta Najeriya (DSPMEAN), ta soki shirin kafa dokar dakatar da fede fatar jaki da sayar da ita a kasashen waje ko kuma dakatar da yanka jakunan.

An kai matakin karatu na biyu a zauren Majalisar Wakilai don tabbatar da dokar a Najeriya.

Shugaban Kungiyar DSPMEAN ta Kasa, Ifeanyi Dike ne ya bayyana haka yayin tattaunawa da manema labarai a Abuja. Ya ce, ana shirin kaddamar da dokar cikin rashin ilimi da yunkurin karya masu sana’ar saye da sayar da jakuna a yankunan karkara.

Dike, ya ce maimakon a kirkiro dokar dakatar da fita da jakuna, kamata ya yi gwamnati ta mai da hankali a kan abubuwan da za su inganta masana’antar da kuma dakatar da safarar jakunan da ake yi wanda hakan yana kawo wa kasuwancin koma baya.

Dike ya kara da cewa, a tsakanin shekarar 2012 da 2018 Najeriya ta yi asarar harajin da ya kai sama da Dala biliyan 2 a duk shekara, wanda adadin ya kai sama da Dala biliyan 7 a shekara shida sanadiyyar safarar jakunan Najeriya zuwa wasu kasashen waje musamman kasar China.

Sakamakon fasahar zamani, kasuwancin jakuna ya yi tasiri sosai, don haka akwai bukatar kara bunkasa shi ta yadda zai taimaka wajen habbaka tattalin arzikin Najeriya.

Wanda ya shiga da shirin aiwatar da dokar dan Majalisar Wakilai daga Jihar Kaduna Garba Muhammed, ya bukaci majalisar ta tattauna batun illar da sana’ar jakunan za ta kawo wa kasa, wanda ya kamata a jiye ta a gefe a kalli baiwar da take tattare da halitta da tarihin da ke ciki da kuma sana’o’in da ake amfana da dabbobin tare da darajar da take tattare da amfani da jakuna a kasar nan.

A cewar Dike, kungiyarsu tana da duk hanyoyin fasahar zamanin na sake haihuwar jakuna da kasuwancinsu da fitar da fatun  zuwa kasashen waje ta yadda ba zai shafi yadda ’yan majalisar suke shirin sanya doka akan batun ba.

Ya bayyana cewa, matsalar safarar jakunan tana da alaka ce da rashin ingantaccen tsari. Ya bukaci gwamnati da ta shirya wani sabon tsarin doka wajen gudanar da kasuwancin jakuna ta yadda ba kowa ba ne zai iya yanka jakuna a kasar nan, don guje wa abin da ake tunani.