‘Najeriya na cikin kasashen Afirka da aka fi mummunan shugabanci’
Najeriya na daya daga cikin kasashen Afirka da suka fi fama da mummunan shugabanci kamar yadda rahoton Cibiyar Nazarin Harkokin Shugabanci a Afirka ta MO Ibrahim (IIAG) na shekarar 2014 da aka gabatar ranar Litinin da ta gabata ya bayyana. Rahoton wanda jaridar Premium Times ta samu kuma ta buga a shekaranjiya Laraba Najeriya tana […]
Najeriya na daya daga cikin kasashen Afirka da suka fi fama da mummunan shugabanci kamar yadda rahoton Cibiyar Nazarin Harkokin Shugabanci a Afirka ta MO Ibrahim (IIAG) na shekarar 2014 da aka gabatar ranar Litinin da ta gabata ya bayyana.
Rahoton wanda jaridar Premium Times ta samu kuma ta buga a shekaranjiya Laraba Najeriya tana da maki 45 da digo 8 kasa da kasha 51 da digi 1 da mafi yawan kasashen Afirka ke da shi, inda ta zo ta 37 a jerin kasashen Afirka 52 a harkokin iya gudanar da mulki.
Kuma Najeriya ta samu maki kasa da yadda galibin kasashen Afirka ta Yamma suke samu wanda ya tsaya kan maki 52 da digo 2, inda ta zo ta 12 a jerin kasashen yankin 15.
Rahoton ya nuna a yayin Najeriya ta samu wannan mummunan matsayi a nazarin IIAG, kasar Mauritius ce ta zo ta daya wajen gudanar da kyakkyawan shugabanci a Afirka inda ta samu maki 81 da digo 7, yayin da Cape berde ta biyo bayanta da maki 76 da digo 6.
Cibiyar IIAG dai tana karkashin Gidauniyar MO Ibrahim (MIF) ce, wadda kungiya ce da ke gudanar da cikkaken nazari da bincike da inganta kyakkywan shugabanci a Afirka.
Kuma tana gabatar da bincike da nazarinta ingantaccen shugabanci a kasashen Afirka duk shekara. Kuma tana tsara dabaru ga ’yan kasa da gwamnatoci da cibiyoyi da sassa masu zaman kansu yadda ya kamata don samar da kyakkyawan shugabanci da gudanar da ayyuka ga jama’a a sassan nahiyar.
Sauran kasashen da suka yi rawar gani sun hada da Botswana wadda ta zo ta uku da maki 76 da digo 2, sai Afirka ta Kudu ta zo ta hudu da maki 73 da digo 3.
kasar Ghana ce ta zo ta bakwai, sai Rwanda ta 11; Benin ta 18, sai Masar ta 26, Mali ta 28, sai Jamhuriyar Nijar ta 29, sai Liberiya ta 31, Kamaru ta 34 da kuma Togo ta 36, dukka suna saman Najeriya mai dimbin arziki da albarkar yawan jama’a.
Najeriya mai sama da mutum miliyan 173, an kiyasta arzikinta na karuwa da kasha 2 da digo 8 a cikin gida, inda take samun Dala biliyan 3013 da digo 3, yayin da take fama da tashin farashin kayayyaki da kashi 2 da digo 8 da kuma karuwar rashin aikin yi da kashi 13 da digo7 duk shekara.
Wani bangare da Najeriya ta fadi kasa, shi ne bangaren tsaro, inda ta zo ta 44 da maki 38 da digo1, sai kiyaye doka da oda ta zo ta 32 da maki 41, wajen tsare amana ta zo ta 30 da maki 36 da digo 6.
A bangaren da ta fadi warwas shi ne na kare rayukan jama’a, inda ta zo ta 49 da maki 16 da rabi, kuma ta kusa da ta karshe a wajen tsaron kasa a matsayin ta 48 da maki 58 da digo 2. A kare hakkin dan Adam ta zo ta 26 bayar da dama a harkokin tattalin arziki ta 31, sai inganta jin dadin dan Adam ta 34.