Najeriya na da hanyoyin samun kudaden shiga sai dai… Sanata Baba-Ahmed
Mene ne mafita ga Najeriya daga faduwar farashin man fetur a kasuwar Duniya?Rashin inganta wasu hanyoyin samun kudaden shiga shi ne babbar matsalar da ke addabar kasar nan a yanzu, tunda farashin man fetur ya fadi warwas a kasuwar duniya, akwai alamun za a sha wuya a bangarori da dama musammna da yake Najeriya na […]
Mene ne mafita ga Najeriya daga faduwar farashin man fetur a kasuwar Duniya?
Rashin inganta wasu hanyoyin samun kudaden shiga shi ne babbar matsalar da ke addabar kasar nan a yanzu, tunda farashin man fetur ya fadi warwas a kasuwar duniya, akwai alamun za a sha wuya a bangarori da dama musammna da yake Najeriya na kokarin ganin ta yi maganin ’yan ta’adda.
Shin ko an hango wannan matsala kafin yanzu?
Abin la’akari shi ne yadda ma’aikatu da hukumomin gwamnati kamar Ma’aikatar Tsare-Tsare ta kasa, ba su yi tanadin irin wannan bakar rana ba. Sun buge ne da dogon Turanci kamar bullo da shirin bunkasa tattalin arzikin kasa a matakin tarayya (NEEDS) da matakan jihohi (SEEDS) da matakan kananan hukumomi (LEEDs), suka manta da idan farashin mai ya fadi, mece ce mafita.
Babban abin darasi a gare mu a yanzu shi ne mu fahimci yadda farashin man fetur ke hawa da sauka. Sannan abin kunya ne a ce Ofishin Babban Mai ba Shugaban kasa Shawara kan Harkar Tattalin Arziki da Ministan Kudi duk sun kasa fihimtar haka tun daga shekarar 1999, a ce sun kasa bambancewa a tsakanin kudin rarar man fetur da kiyasin kudin man fetur dangane da tattalin arzikin kasa.
Ya dace ne su fahimci bambancin ne tun kimanini shekara goma sha biyar da suka wuce domin yin maganin wannan kalubale ga tattalin arzikin kasa.
Wani abin ban haushi shi ne yadda ba mu da wani asusu na ko-ta kwana saboda irin wannan lokaci. Da a ce akwai wannan shiri to da ba a shiga wannan hali na ha’ula’i ba.
Mene ne mafita a yanzu?
An riga an yi kura-kurai da yawa. Ya dace gwamnati ta zamo mai hangen nesa. Sannan ya kamata kada a firgita domin in an yi haka, to ana iya kara yin wani kuskuren da bai dace ba in farashin ya kai Dala 100 ga kowace gangar danyen man fetur domin kada mu koma ’yar gidan jiya. Ba wai ba inke gwmanatin kirki ita ce mafita, kuma ba za a iya samun nasara a kara samun hanyoyin kudaden shiga ba har sai an kuma samar da ilmi mai inganci. Wato gwamnati mai inganci ce kadai ke samun karin kudaden shiga ba ’yan handama da babakere ba.
Shin kana ganin ana kan hanyar inganta tattalin arzikin kasar nan?
Kawar da gwamnatin da ta wuce na daya daga cikin shirin. Sai kuma wannan gwamnati ya dace ta kara jan damara domin fitar da kitse daga wuta cikin gaggawa musamman samar wa matasa da ilimi ingantacce, ba kawai samar da takardar shaidar digiri ko mai kama da haka ba, sai dai misali ko manomi da ke noma ya samu ilimin inganta harkar noma da kayan zamani da samun ingantattun iri da samun rance mai sauki. Kuma gwamnati ta daina yin dogon Turanci a matsayin wai shi ne ci gaba. An tsaya a san me muke so mu ya kamata mu samu. Sannan a yi kiyasin me aka nomawa a shekara kuma akwai rara ko babu. A lura cewa tun samun ’yan cin kanmu har yau muna daukar kaya ne a loda a mota a kai, kamar yadda muke ganin leburori na yi a tsakiyar birnin Abuja. Yaushe za mu fara amfani da kura da kuma katafila don yin haka? Akwai aiki a gaban Najeriya.
Wace shawara za ka ba Shugaba Muhammadu Buhari?
Ya kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya gyara harkar sayen kayayyakin gwamnati domin ana satar kudi rututu ta wajen. Idan an kashe Naira biliyan daya, to a tabbatar an kawo akalla kashi casa’in na kayan, ba kashi goma ba. Domin za ka an yi ginin gwamnati da aka kasha Naira biliya guda, in ka duba sai ka ga bai wuce a ce an kashe Naira miliyan dari a aikin ba.