Najeriya na da matukar karancin ‘yan sanda – Usman Bello Kumo

Dan Majalisar Wakilai Usman Bello Kumo, shi ne Shugaban Kwamitin Harkokin ’Yan sanda a majalisa ta 7 kuma shugaban kwamitina yanzu. A tattaunawar da ya yi da Aminiya, ya yi tsokaci kan batutuwan da suka shafi aikin ’yan sanda da hanyoyin da yake ganin in an bi za a inganta aikin ’yan sandan. Ya kuma […]

Najeriya na da matukar karancin ‘yan sanda – Usman Bello Kumo

Alhaji Usman Bello Akko

Dan Majalisar Wakilai Usman Bello Kumo, shi ne Shugaban Kwamitin Harkokin ’Yan sanda a majalisa ta 7 kuma shugaban kwamitina yanzu. A tattaunawar da ya yi da Aminiya, ya yi tsokaci kan batutuwan da suka shafi aikin ’yan sanda da hanyoyin da yake ganin in an bi za a inganta aikin ’yan sandan. Ya kuma yi bayani game da dambarwar da ake yi kan wasu batutuwa da suka shafi shugabancin majalisar:

 

Me za ka ce game da nasarar da ka samu, a kotun zabe dangane da abin da ya shafi cikin jam’iyyarku ta APC, amma PDP ta shigar da kara a kai?

Alhamdulillah, nasara ko akasin haka duk daga Allah ne, kuma jarrabawa ne dukkansu. Don haka nasarar da na samu ba ma kawai a kotun sauraron kararrakin zabe ba, a’a an kai karata a Babbar Kotun Tarayya kan al’amuran da suka shafi gabanin zabe, na yi rashin nasara, sai na daukaka kara zuwa Kotun Daukaka Kara ta Jos, inda na yi nasara. Sun daukaka kara zuwa Kotun Koli kuma can ma Allah Ya ba ni nasara. Sai kuma aka sake kai ni kara a Kotun Kararrakin Zabe, nan ma Allah Ya taimake ni. Korafin da aka gabatar a kaina gabanin zabe, shi ne ’yan Jam’iyyar PDP suka sake gabatarwa a kotun zabe. Amma sai kotun ta ce musu ai wannan batu ne da ya shafi cikin-gida (jam’iyyarmu ta APC) don haka ba su da hurumin magana a kai, kamata ya yi su kai karar gaban babbar kotu, don haka sun rasa karar.

Wadanne shirye-shirye kake da su a majalisa ta 9, kasancewar ka taba wakiltar Akko a baya, kuma wadansu na ganin ba ka tabuka abin a zo a gani ba? 

Ba gaskiya ne ba. Mun gina cibiyoyin kiwon lafiya a Bula da Taliyawa da Kembu, a matsayin ayyukan mazabu. Akwai kuma wanda ba mu karasa gininsa ba a Gujba, kuma insha Allah za mu karasa. Akwai ayyukan burtsatse masu aiki da hasken rana da makarantu tare da samar da cibiyoyin koyon sana’a da dama. Insha Allah, yanzu da yake mun kara samun dama, za mu yi amfani da gogewar da muka samu a baya wajen samar wa al’umma ababen da suke bukata. Kuma amincewar da jama’a suka yi mini ne ya sa suka sake ba ni damar wakiltarsu. Mun sama wa matasa masu dimbin yawa ayyukan Imigireshan da soja da Kwastam da dan sanda. Kuma da yake Allah Ya sake ba ni damar shugabantar Kwamitin Ayyukan ’Yan sanda, insha Allah, za mu yi adalci ga kowane bangaren kasar nan; kuma  mazabata da Jihar Gombe za su amfana sosai da wannan mukami.

Garin Kumo na da masana’antar sarrafa Tumaturin gwangwani da ta durkushe, akwai wani shiri da kake da shi na jawo hankalin gwamntin Jihar Gombe ko kawance da kamfanonin noma da zimmar farfado da kamfanin, don samun kudaden shiga da samar wa matasa aiki?

Abin da zan yi a nan bai wuce in shawarci wadanda abin ya shafa ba; musamman ma Gwaman Jihar Gombe, wanda shi ma yake da kyakkyawar niyya ta fuskar haka. Kuma kasancewar Gombe jihar manoma ce, za mu yi amfani da damar wajen warware ababuwan da ke kawo kiki-kaka da Jihar Bauchi game da kamfanin; saboda an samar da Jihar Gombe ce daga tsohuwar Jihar Bauchi. Kuma farfado da kamfanin zai zama mai matukar alfanu ga gwamnatin jihar da al’ummar da kamfanin yake yankinsu.

Yaya aka yi kuka samu nasarar kwatar mulki daga hannun Jam’iyyar PDP wadda ta shafe shekara 16 tana jan zarenta a Jihar Gombe?

Ina ga yin aiki tare ya taimaka sosai. Kasancewata daya daga cikin masu hadaka da sauran wadanda hankalinmu ya zo guda, mun yi aiki tukuru wajen kwatar mulki daga PDP a Gombe. Dadin dadawa, mun yi amfani da damar rashin iya mulki, da rashin yin amfani da kudaden gwamnati yadda ya kamata tare da sassaucin ra’ayi irin na tsohuwar gwamnatin sun taimaka mana. Kuma shi tsohon Gwamnan bai san madafarsa ba; don haka sai muka yi amfani da dabarunmu na ’yan siyasa muka tumbuke jam’iyyar daga mulki.

Ko kana ganin za a samu yaukin dangantaka a tsakanin Bangaren Zartarwa da na Majalisa, lura da zaman ’yan marina da bangarorin biyu suka yi a baya?

Kwarai kuwa, za a samu. Abin da ke faruwa ko a kasashen da suka ci gaba shi ne aiki tare a tsakanin wadannan bangarorin biyu. Ba wai yaki ba ne, saboda akwai tanadin daunin iko a tsakaninmu da ba zai saka muna samun sabani ba. Kawai za mu yi musayar hikimomi ne tare da muhawara a kan batutuwan da wasu mu hadu a kansu wasu kuma mu saba. Aikin zartarwa shi ne su aiwatar tare da kashe kudaden kasafi; mu kuma mu sahale kasafin. Dukkanmu muna aiki ga ’yan Najeriya ne kuma amanarsu na wuyanmu. Don haka ina ganin fahimtar juna tare da aiki tare zai taimaka wajen wajen zaburar da ayyukan ci gaban kasa.

Wadansu ’yan Najeriya na cewa lokaci ya yi na a soke kudaden raya mazabu da ake ba ku, saboda wani rahoto da aka fitar da ya nuna an kashe fiye da Naira tiriliyan biyu tun shekarar 2000, amma kusan babu ayyuka a mazabun. Mene ne ra’ayinka?

Kowa yana da nasa ra’ayin. Mu wakilan jama’a ne, kuma babu mazabar a Najeriya da ba ta da wakilci a majalisun tarayyar nan biyu. Duk abin da muke samu ai ba gidajen iyayenmu muke kai shi ko kuma aljifanmu ba; muna kai su wadannan mazabu ne, kuma su ne Najeriyar. Abin da ya kamata ’yan Najeriya su gane kan ayyukan raya mazabu shi ne, kawai saka ayyukan a kasafin kudi shi ne aikin majalisa; amma aiwatar da shi kuma bai rataya kan majalisa ba. Amma ina ganin, da an wayar da kawunan ’yan Najeriya game da hakan, to kuwa da za su yi kiran lallai a ci gaba da hakan.

Me za ka ce game da cewa shugabannin majlisun tarayyar nan biyu, duk ’yan amshin shatan bangaren zartarwa ne, ko ba su cancanci rike mukaman ba?

Ba wani mahaluki mai hankali da zai ce wai ba su da kwarewa. Shugabannin Majalisar  Dokokin suna da gogewa a harkar majalisa na shekara 30, inka hada su duka biyu. Femi ya shafe fiye da shekara 20 a harkar majalisa, shi kuma Wase yana da gogewa na shekara 16, sai kawai ka ce musu ba su da gogewa, ban yarda ba. Ya za a yi su zama karnukan farautar wani, bayan masu ilimi ne sun yi karatu a jami’a, sun ci zabe kimanin sau shida ga kuma tarin gogewarsu. Kawai soki-burutsun ’yan siyasa ne. Amma karan Femi da Wase ya kai tsaiko, a ko’ina a duniyar nan a dai fagen majalisar dokoki.

Kasancewar an nada ka Shugaban Kwamitin Ayyukan ’Yan sanda kuma ka taba rike mukamin a baya, lura da kalubalen tsaro a Najeriya, me kake ganin ya kamata gwamnati ta yi wajen inganta rundunar ’yan sanda don gudanar da ayyukanta na tabbatar da tsaron kasa?

Shawarata a nan ita ce, gwamnati ta tsunduma daukar aikin dan sanda sosai da sosai, sakamakon yadda rundunar ke matukar fuskantar karancin ma’aikata tare da karancin kudaden aiki. Kawai gwamnati ta sake duba kan kasafin kudin ’yan sandan. A tsarin aikin dan sanda na duniya, shi ne kowane dan sanda guda ya lura da mutum biyar. Amma dubi abin da ke faruwa a Najeriya, inda muke da yawan al’umma kimanin miliyan 200, amma ’yan sandanmu ba su wuce dubu 372 Sun yi matukar karanci. Don haka shawarata ga gwamanti don magance matsalar tsaro kawai ta fara daukar aikin ’yan sanda babu kakkautawa a-kai-a-kai. Muna da dumbin matasa majiya karfi da suka yi karatu amma babu aikin yi, marar aikin yi kuma an ce Shaidan ne abokinsa. Ina shawartar gwamnati a kowace shekara ta dauki ’yan sanda kimanin dubu 40 zuwa dubu 50, hakan zai taimaka. Kuma idan an dibi ’yan sanda, to a maida su jihohinsu su yi aiki a can, saboda sun nakalci lungu da sakon wurarensu, hakan zai taimaka wajen tattara bayanai don shawo kan matrsalar tsaro.

Me ya kamata gwamnati ta yi wajen farfado da kimar aikin ’yan sanda?

Ta kara musu kasafin kudi. Ta kuma ba su horo a-kai-a-kai, tare da sauya tunaninsu, don ya yi daidai da na duniya.

Kana da ra’ayin samar da ’yan sandan jiha ne kawai mafita kan halin tabarbarewar tsaro a kasa?

Eh, ai abin da ke faruwa a dukkan kasashen duniya. Dama aikin ’yan sanda shi ne aiki da fararen hula, don haka samar da ’yan sandan jihohi abu ne mai kyau.

Mene ne ra’ayinka game da mayar da ’yan N-Power zuwa masu aikin taimaka wa ’yan sanda a yankunansu da Gwamnatin Tarayya da gwamnonin kasar nan ke shirin yi?

Daidai ne hakan. Ko me ka kira shi ai in dai zai taimaka wajen inganta aikin tsaro tare da yaki da matsalar tsaro, ni ma ra’ayina ke nan. Abin da muke bukata shi ne samar da zaman lafiya a Najeriya; wanda hakan zai zaburar da habakar tattalin arziki.