Najeriya na dab da fuskantar karancin iskar da mutane ke shaka – Masani

Ya ce muddin ba a yi wa tufkar saran itatuwa hanci ba, Najeriya na cikin tsaka mai wuya.

Najeriya na dab da fuskantar karancin iskar da mutane ke shaka – Masani

Wata mata tana shakar numfashi Hoto: Seattle Times

Wani kwararre a kan harkar muhalli, Mista Azibaola Robert, ya koka kan yadda ake yawan sare bishiyoyi a Najeriya, inda ya ce hakan na babbar barazana ce ga iskar da mutane da dabbobi ke shaka.

Masanin ya bayyana hakan ne ranar Asabar lokacin da yake jawabi ga manema labarai yayin wani taron kwana 14 na nuna wani faifan bidiyo kan muhalli da ke gudana a garin Otakeme na Karamar Hukumar Ogbia ta Jihar Bayelsa.

A cewarsa, muddin ba a yi wa tufkar saran itatuwa barkatai hanci ba, akwai yuwuwar Najeriya ta fuskanci karancin iskar da mutane ke shaka ta Oxygen, nan ba da jimawa ba.

Mista Azibaola ya ce abin takaici ne yadda saran bishiyoyi ba tare da ana dasa wasu ba yake barazana ga manyan dazukan da ke yankin Neja Delta, wanda ya ce tuni ma ya fara shafar muhalli.

Ya ce, “Muna kokarin nuna wa jama’a illar da ke tattare da sare bishiyoyi. Mutane na sare bishiyoyin da ke kare muhalli kuma su bamu iskar da muke shaka.

“Babu wata doka da take yaki da wannan dabi’ar a yankin Neja Delta da ma Najeriya baki daya. Saboda haka, akwai babbar barazanar da take tunkaro mu, muddin ba mu yi wani abu ba.

“Ba mu taba yunkurin gano kason iskar da muke shaka daga bishiyoyi ba, kawai mun mayar da hankali muna ta sare su ba kan gado,” inji shi.

Ya ce an shirya taron ne don a fito da yanayin muhallin Najeriya, musamman ma na yankin Neja Delta, domin a fadakar da mutane kan albarkatun da Allah ya hore wa kasar, wadanda ya ce akasarinsu ba a ma amfani da su.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno