Najeriya na fama da mashako – Sarkin Musulmi

Shugaban Majalisar Sarakunan Arewa Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, ya ce Najeriya tana fama da mashako, kuma babu abin da yake tafiya daidai tare da gargadin shugabannin siyasa su dakatar da kamfe din cin zarafi da bata suna. Sarkin Musulmi ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi wajen taron majalisar a […]

Najeriya na fama da mashako – Sarkin Musulmi
Najeriya na fama da mashako – Sarkin Musulmi

Shugaban Majalisar Sarakunan Arewa Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, ya ce Najeriya tana fama da mashako, kuma babu abin da yake tafiya daidai tare da gargadin shugabannin siyasa su dakatar da kamfe din cin zarafi da bata suna.

Sarkin Musulmi ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi wajen taron majalisar a Kaduna a shekaranjiya Laraba, inda ya ce wajibi ne sarakuna su fada wa shugabannin siyasa gaskiya saboda sun san abin da jama’arsu suke so, kasancewar sun fi kusa da su. Ya ce a matsayinsu na mutane ya wajaba ’yan siyasa su rika mutunta juna ba koyaushe su rika kallon zabe a matsayin abin a mutu ko a yi rai ba.
“Tilas mu fada wa shugabannin siyasa gaskiya, bai dace mu zuba ido abubuwa suna tafiya ba daidai ba, amma mu rika cewa komai na tafiya daidai. Ina shaida muku abubuwa ba su tafiya daidai a kasar nan, don haka ya rage namu mu taimaki shugabanninmu su koma kan gaskiya ta yadda Arewa za ta ci gaba, Najeriya ta ci gaba ta zama mai karfi, kuma wajibi ne mu rika magana kan batutuwan da suke addabara kasar nan, bai dace mu yi shiru ba. Akwai dimbin cin hanci da rashawa da dimbin kama-karya da yawan kashe-kashe. Abin da ke faruwa a Arewa maso Gabas babban abin takaici ne,” inji Sarkin Musulmi.
Sarkin Musulmin ya bukaci sarakuna da ’ya siyasa su fifita bukatun kasa a kan bukatunsu na kashin kai. “Mutane suna da yakini a kan mu sarakuna fiye da yadda suke da shi a kan ’yan siyasa, wajibi ne mu guje wa abin da ya faru a shekarar 2011 a wannan zabe na 2015, domin na san bisa kuskure an zarge mu da goya wa wata jam’iyyar siyasa baya. Na ce, KUSKURE da babbar murya, amma idan ka yi kuskure mala’iku dubu suka ce daidai ne da bambanci, don haka mu lura. Mu kauce wa yin kuskure, kuma ina da yakinin za mu rika yin abin da yake daidai. Mu koma mu kalli abin da kakanninmu suka yi, mu yi koyi da su domin mun fito ne daga al’adu da dabi’u da addinai daban-daban, amma duk da haka al’umma guda ce da za mu samu daukaka ta hanyar hadin kai don haka wajibi ne mu tsayu wajen tabbatar da hadin kai a tsakaninmu saboda hakan yana da muhimmanci,” inji shi.