Najeriya na kan turbar samun ci gaba mai ɗorewa — Tinubu

Shugaban ya buƙaci ‘yan Najeriya su dage wajen yi wa shugabanninsu addu’a.

Najeriya na kan turbar samun ci gaba mai ɗorewa — Tinubu

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su yi wa shugabanninsu addu’a tare fatan samun ci gaba mai ɗorewa a ƙasar.

Wannan na cikin saƙon Kirsimeti da shugaban ya aike wa Kiristoci yayin da suke shirye-shiryen gudanar da bikin Kirsimeti na bana.

“Kirsimeti na tunatar da mu ƙaunar Ubangiji, zaman lafiya, da haɗin kai,” in ji Tinubu.

“Tana nuna mana cewa ci gaba zai iya bayyana duk da ƙalubalen da muke fuskanta.

“Yayin da muke bikin, mu tuna da waɗanda ke cikin wahala saboda munanan al’amura da suka faru kwanan nan kuma mu yi addu’a don samun lafiya da kwanciyar hankali.”

Ya nuna damuwarsa kan waɗanda suka rasa rayukansu a turmutsitsin da ya faru a Ibadan, Okija, da Abuja.

“Muna addu’a irin waɗannan munanan abubuwan ba za su sake faruwa ba,” in ji shi.

Shugaban ya kuma yi kira da a tausayawa waɗanda ke cikin ƙunci a wannan lokaci, tare da yaba wa sadaukarwar sojojin Najeriya.

“Sojojinmu da suke kare ƙasarmu sun cancanci goyon baya da addu’o’inmu,” in ji Tinubu.

“Tare, za mu iya sake gina Najeriya mai albarka.”

Tinubu ya yi wa matafiya fatan alheri, inda ya ce gwamnatinsa ta samar da jiragen ƙasa kyauta da rangwamen kuɗin sufuri a faɗin ƙasar domin sauƙaƙa tafiye-tafiye.

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF

Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Babiana

An horar da mutum 500 dabarun adana ruwa don inganta muhalli a Gombe