Najeriya na kashe fiye da biliyan 300 wajen shigowa da shinkafa – CBN
Binciken da babban bankin Najeriya ya gudanar ya nuna cewa ana kashe zunzurutun kudi har naira biliyan 364 wajen shigowa da shinkafa kasar nan. Batun hakan ya fito ne ta bakin wani jami’in bankin na CBN Malam Baba Isah, a lokacin taron kungiyar manoma ta kasa AFAN na shiyyar Arewa maso Gabas da suka gudanar […]
Binciken da babban bankin Najeriya ya gudanar ya nuna cewa ana kashe zunzurutun kudi har naira biliyan 364 wajen shigowa da shinkafa kasar nan. Batun hakan ya fito ne ta bakin wani jami’in bankin na CBN Malam Baba Isah, a lokacin taron kungiyar manoma ta kasa AFAN na shiyyar Arewa maso Gabas da suka gudanar a Gombe.
Ya ce Najeriya ita ce kasa ta biyu a duniya wajen shigowa da abinci kasashensu daga kasashen ketare. Malam Baba Isah, ya kara da cewa ana kashe kimanin naira biliyan 364 wajen shigo da shinkafa naira biliyan 217 wajen shigo da sukari sai naira biliyan 635 wajen shigo da alkama sannan naira biliyan 97 wajen shigo da kifi.
Ya kuma ce babban bankin ya bullo da shirye-shirye masu yawa ne saboda a inganta harkar Noma a kasar dan cike wannan gibi wanda kuma hakan ya yi tasiri wajen rage kashe kudin. Da yake jawabi, Kwamishinan aikin gona na jihar Gombe, Alhaji Dahiru Buba Biri, ya ce harkar Noma ya ja baya a kasar nan musamman a jihar Gombe, amma yanzu an farfado da shi. Dahiru Buba Biri, ya ce kungiyar Manoma ta kasa AFAN tana kokari wajen kawo canji a harkar Noma dan haka ya kiraye su da kara ninka kokari wajen hada gwiwa da bankin CBN dan bunkasa harkar Noma. Ya kuma ce a Jihar Gombe gwamnatin Dankwambo ta yi kokari wajen bai wa harkar noma kulawa dan shi ne abunda yake kawo kudin shiga kullum. Daga nan sai ya jinjinawa bankin Najeriya CBN na yadda ya bullo da bangarori daban-daban dan taimakawa harkar Noma a fadin kasar nan.
Mista Bitrus Haruna, daga bankin Manoma BOA wanda ya wakilci babban Daraktan Bankin ya bayyana cewa harkar noma harkar ce mai muhimmanci da take rage zaman banza a tsakanin matasa. Mista Bitrus Haruna, ya ce Bankin CBN ya bullo da shiri kan Noma wanda kuma ya samu karbuwa daga gwamnatin tarayya wanda kuma zai ci gaba da karbuwa.
Ya koka kan yadda ake bai wa manoma rancen noma amma ba sa son biya dan wasu ma su amfana. Daga nan sai ya ce Bankin Manoma ya fitar da kudi kimanin naira biliyan 43 dan manoma amma abun takaici an bar shiyyar Arewa maso Gabas a baya, inda kwata-kwata bai kai biliyan 1 da miliyan dari biyar ba suka amfana dashi inda ya ce gara a farka.
Kwamishinan aikin gona na jihar Adamawa, wanda ya samu wakilcin Mista Numara Bagara, cewa ya yi yanzu haka a jihar Adamawa tuni sun yi wa manoman rani dubu 10 rijista dan shirye-shiryen fara noman rani. Daga nan sai ya ce suna samun hadin kan hukumar inshoran aikin gona ta NAIC na yadda suke taimakawa manoman su idan suka samu asara a harkar noman nasu. Taron na shiyyar arewa maso gabas ya samu halartar shugabanin kungiyar manoma na AFAN na jihohi shida na yankin da kuma Mataimakin shugaban na kasa, Auwal Bamanga Tukur.